Kada ka cire takunkumin hana shigo da shinkafa, gwamnan Benue ya bukaci Buhari

Kada ka cire takunkumin hana shigo da shinkafa, gwamnan Benue ya bukaci Buhari

- Gwamnan jihar Benue ya mika babbar bukata gaban shugaba Muhammadu Buhari

- Gwamna Ortoma ya bukaci shugaban kasa kada ya cire takunkumin hana shigo da shinkafa daga waje

- Ortom ya lissafa abubuwan da aka ribatu da su sakamakon sanya takunkumin tsawon shekara daya da yan watanni

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari kada ya saurari maganan mutane na cire takunkumin hana shigo da shinkafar gwamnati daga kasashen waje.

The Punch ta ruwaito cewa gwamna Ortom ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ranar Litinin, 30 ga Nuwamba.

Ya yabawa shugaba Buhari kan dokar yayinda ya ambaci muhimman riba biyu da aka ci tun lokacin da aka hana shigo da shinkafa.

A cewar gwamna Ortom, hana shigo da shinkafa ya harzuka manoman shinkafan gida da kuma noma gaba daya a jihar.

Ya ce wannan ne abu guda babba da gwamnatin Buhari tayi.

Gwamnan ya bayyana cewa duk da cewa za'a fuskanci matsaloli da wahala na dan lokaci, manoma na samun kudi sosai yanzu fiye yadda suke samu a baya.

Wani dalilin da gwamnan ya ambata shine samarwa matasa aikin yi. Ya ce matasa da dama sun koma noma kuma hakan ya taimaka.

Ortom ya ce idan aka cigaba a haka, jihar Benue za ta rika samawa kasar gaba daya abinci.

KU KARANTA: Gwamna jihar Yobe kwana uku yake a jiharsa, daga Abuja yake mulki

Kada ka cire takunkumin hana shigo da shinkafa, gwamnan Benue ya bukaci Buhari
Kada ka cire takunkumin hana shigo da shinkafa, gwamnan Benue ya bukaci Buhari Hoto: @GovSamuelOrtom
Asali: Facebook

KU DUBA: Yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna diban mutane, Sarkin Musulmi

A bangare guda, manoman Najeriya a ranar Laraba sun yi Alla-wadai da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na sake bude iyakokin Najeriya na kasa.

Sun bayyana cewa bude iyakokin a yanzu da kayan abinci ke hauhawa abune mai hadarin gaskiya.

Sun ce kasashe makwabta da suka dogara kan Najeriya wajen samun kayan abinci zasu shigo kasar kuma hakan zai sa kayan abinci ya sake hauhawa, Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel