Abin da ya hana Pius Anyim da wasu ‘Yan Majalisa shiga APC tare da Gwamna Dave Umahi

Abin da ya hana Pius Anyim da wasu ‘Yan Majalisa shiga APC tare da Gwamna Dave Umahi

-David Umahi yace ya tsara barin PDP ne tare da irinsu tsohon SGF, Anyim Pius Anyim

-Gwamnan ya ce hakan bai yiwu ba saboda ya je sun yi zama da shugaban kasar shi kadai

-Anyim Pius Anyim ya musanya zargin, yace gwamnan yana neman hanyar hallaka shi

A ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba, 2020, gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya yi karin haske game da sauyin-shekar da ya yi zuwa APC.

David Umahi ya ce ya tsara barin jam’iyyar APC ne tare da tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Anyim Pius Anyim da wasu ‘yan majalisa.

Jaridar The Nation ta ce gwamnan ya bayyana wannan ne a wajen taron masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC na jihar Ebonyi da aka yi a Abakaliki.

A cewar gwamnan, daga baya ne Sanata Anyim Pius Anyim wanda ya rike kujerar sakataren gwamnatin Goodluck Jonathan ya fita daga shirin.

KU KARANTA: AESID ta na so 'Yan Majalisa su tunbuke Umahi

David Umahi ya ke cewa Anyim Pius Anyim bai koma APC ba ne saboda an ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari ba tare da an tafi da shi ba.

Umahi ya ce sun tsara cewa bayan ya koma APC, sauran ‘yan majalisar tarayyan jihar zasu biyo shi, a karshe gwamnan kadai ne ya tattara ya bar PDP.

Umahi yace Anyim ya sa ya tattago bashin Naira biliyan 5 saboda PDP ta lashe zaben 2015, ya ce sai da ya saida wasu kadarorinsa ya iya biyan bashin

Anyim Pius Anyim ya maida martani, ya na mai zargin gwamnan na Ebonyi da neman ganin bayansa saboda ya ki amincewa da maganar shiga APC.

KU KARANTA: Za a binciki Shugaban APC da laifin kitsawa jam’iyya zagon-kasa

Abin da ya hana Pius Anyim da wasu ‘Yan Majalisa shiga APC tare da Gwamna Dave Umahi
Pius Anyim ya sa Umahi ya ci bashi saboda nasarar PDP Hoto: www.thecable.ng
Source: UGC

Sanata Anyim Pius Anyim ya sanar da shugaban kasa, IGP da DSS cewa akwai yunkurin da ake yi a kashe shi don kurum ya ki sauya-sheka daga PDP.

Tsohon Sanatan ya ce Umahi ne ke neman kashi ba kowa ba, tun da ya ki karbar tayin shiga APC.

A baya kun ji cewa sauyin-shekar Dave Umahi ta sa Bello Matawalle na jihar Zamfara ya fara hangen ya yi watsi da tafiyar jam'yyar APC, ya koma APC.

A halin yanzu kafar gwamnan na Zamfara daya ta bar jam’iyyar PDP, ta tsallaka zuwa APC, sai dai gwamna Matawalle zai gamu da cikas idan har ya bar PDP

Rade-radi sun ce Gwamnan ya shirya barin PDP, amma manyan jam’iyya suka shawo kan shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel