Kisan manoma 43 a Zabarmari: Zahra Buhari ta yi martani
- Zahra Buhari ta bayyana alhininta a kan kisan manoman Zabarmari
- A cewarta, zuciyarta tana zubar da jini saboda takaicin al'amarin
- Ta yi wannan wallafar ne bayan kwana 2 da aukuwar lamarin
Zahra Buhari-Indimi, diyar shugaba Muhammadu Buhari, ta wallafa hoton wata jarida mai dauke da hotunan kashe-kashen Zabarmari kuma ta rubuta: "Zuciyata tana zubar da jini".
Zahra Buhari ta bayyana alhininta a kan kashe-kashen manoman jihar Borno da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka yi.
Ta yi wannan wallafar ne bayan kwanaki 2 da 'yan Boko Haram suka kai wa manoman shinkafa hari, suka yi musu yankan rago.
KU KARANTA: Tashan wutan lantarki ta kasa ta lalace, sunayen jihohin da rashin wuta zai shafa
Da farko an ce gabadaya yawan wadanda aka kashe guda 43 ne, amma daga bisani aka tabbatar da cewa mutane 110 ne, kamar yadda majalisar dinkin duniya ta sanar.
KU KARANTA: Turmi da tabarya: Matashi mai shekaru 19 ya mutu a kan karuwa a Legas
A wani labari na daban, duk gwamnonin jihohi 36 da ke karkashin NGF sun bayyana takaicinsu a kan kisan manoma 43 da aka yi a jihar Borno ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba.
A wata takarda da suka saki a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba, wacce shugaban kungiyar, Gwamna Kayode John Fayemi na jihar Ekiti ya fitar, ya ce kisan zaluncin da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka yi, yana nuna zalunci da munin hali irin nasu.
Fayemi ya ce kisan zaluncin yana nuna tsananin gazawar tsaro a Najeriya, domin hakan yana nuna kasawar jami'an tsaro wurin kulawa da rayukan jama'a.
Kisan ya matukar girgiza zukatan jama'a a fadin duniya. Kasar Saudi Arabia da Amurka sun yi Allah-wadai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng