Zabarmari: Tambuwal da Zulum za su hada kai don gano mamata
- Gwamna Aminu Tambuwal ya yi martani a kan kisan kiyashin da yan Boko Haram suka yi wa manoma a yankin Zabarmari da ke Borno
- Tambuwal ya nuna damuwa da bakin ciki a kan wasu yan jihar Sokoto da aka kashe a harin bayan sun je neman halaliyarsu a jihar
- Ya kuma sha alwashin hada karfi tare da Gwamna Babagana Zulum don gano sauran mamatan da bayar da tallafi ga iyalinsu da wadanda suka jikkata
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya nuna aihini da damuwa a kan kisan kiyashin da mayakan Boko Haram suka yi wa wasu yan jiharsa a Borno.
Tambuwal ya bayyana wannan farmaki a matsayin ta’asa mafi muni da cin amana ga yan jihar da suka tafi neman halaliyarsu, jaridar Aminiya ta ruwaito.
Har ila yau gwamnan ya kuma yi alkawalin hada kai da Gwamnatin Babagana Zulum na jihar Borno domin ganin an gano yawan ’yan asalin jihar da suke cikin wadanda aka yi wa kisan gillar.
KU KARANTA KUMA: Tawagar FG sun isa Borno a kan kisan manoma 43 da Boko Haram tayi
Ya kuma bayyana cewa zai bayar da tallafin gaggawa ga wadanda suka jikkata tare da taimaka wa iyalan mamatan.
Tambuwal ya nemi a kara tsaurara matakan tsaro da kuma bin hanyoyin da ya kamata wajen kawo karshen wannan matsala don ceto rayuka da dukiyoyin al’umma.
A wata takarda da ya fitar wadda ya sanyawa hannu da kansa aka raba wa manema labarai, Tabuwal ya yi addu’ar samun rahama ga mamatan.
A gefe guda, gwamnonin jihohi 36 da ke karkashin NGF sun bayyana takaicinsu a kan kisan manoma 43 da aka yi a jihar Borno ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba.
A wata takarda da suka saki a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba, wacce shugaban kungiyar, Gwamna Kayode John Fayemi na jihar Ekiti ya fitar, ya ce kisan zaluncin da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka yi, yana nuna zalunci da munin hali irin nasu.
Fayemi ya ce kisan zaluncin yana nuna tsananin gazawar tsaro a Najeriya, domin hakan yana nuna kasawar jami'an tsaro wurin kulawa da rayukan jama'a.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng