Abin ya wuce mutane 40, manoma 110 aka yi wa kisan gilla a Zabarmari inji UN

Abin ya wuce mutane 40, manoma 110 aka yi wa kisan gilla a Zabarmari inji UN

- Adadin manoman da Boko Haram ta kashe a Borno ya zarce yadda ake tunani

- Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce fiye da mutum 100 ne ‘Yan ta’addan suka kashe

- A ranar Asabar, an bizne mutum 40 da ‘Yan Boko Haram suka yi wa kisan gilla

Sababbin alkaluma sun bayyana game da adadin mutanen da aka hallaka a garin Zabarmari da ke jihar Borno, a Arewa maso gabashin Najeriya.

Kamar yadda mu ka samu labari daga RFI Hausa, adadin manoman da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram suka kashe ya haura mutane 70.

A wani kaulin, an tabbatar da cewa mutanen da aka yi wa yankan rago sun zarce wannan adadi.

KU KARANTA: An tsige shugaban bataliyar sojoji bayan harin Zabarmari

Majalisar dinkin Duniya watau UN ta ce kimanin mutane 110 ne aka rasu a wannan mummunan hari da ‘yan ta’addan na Boko Haram suka kai.

UN ta bada sanarwa ne ta bakin mai kula da ayyukanta na jin-ƙai, Mista Edward Kallon, wanda ya bayyana wannan sabon hari da tashin hankali.

BBC Hausa ta bayyana cewa majalisar dinkin Duniyar ta bada wannan sanarwa ne a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba, bayan bizne mamatan.

Da farko rahoton da ya zo shi ne mutum 40 zuwa 43 aka rasa a sanadiyyar wannan hari da ‘yan ta’adda suka kai wa manoma a kusa da Maiduguri.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun yiwa manoma yankan rago a jihar Borno

Abin ya wuce mutane 40, manoma 110 aka yi wa kisan gilla a Zabarmari inji UN
Farfesa Babagana Umara Zulum wajen jana'iza Hoto: Twitter.com/GovBorno
Asali: Twitter

A tashi guda an bizne mutane kimanin 40, inda gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum da hannunsa ya rika daukar gawa a makara.

Bayan jana’izar wadanda suka riga mu gidan gaskiya, Babagana Umara Zulum, ya nemi Duniya ta kawo wa Borno agaji a kan ta’adancin Boko Haram.

A baya kun ji cewa Mai girma Gwamna Babagana Zulum ya jagoranci jana'izar manoman da Boko Haram tayi wa yankan rago a Zabarmari da ke jihar Borno.

Bayan an hallaka wadannan Bayin Allah a daren ranar Asabar, jama'a sunce ba za suyi masu sallah ba sai a idanun gwamna, kashegari ya dura garin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng