Jama’an da suke Arewa su kare kansu daga Boko Haram da Miyagu – Kungiyar CNG

Jama’an da suke Arewa su kare kansu daga Boko Haram da Miyagu – Kungiyar CNG

- Kungiyar CNG ta yi magana game da mugun harin da aka kai a garin Zabarmari

- CNG ta ce sha’anin rashin tsaro yana ta kara ta’azzara ne a yankin jihohin Arewa

- Kungiyar take cewa ya zama dole yanzu mutanen yankin su tashi, su kare kansu

Bayan an kai wa wasu Bayin Allah hari a garin Zabarmari, jihar Borno, an ga bayan rayuka 43, wata kungiya mai suna CNG, ta fito ta yi magana.

Gamaryyar kungiyoyin Arewa ta CNG ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohi sun gaza kare rayukan al’umma.

Da take magana game da harin, CNG ta bakin mai magana da yawunta, Abdul-Azeez Suleiman, ta ce gwamnati ba za ta iya kare ran mutanen Arewa ba.

KU KARANTA: Kungiyar 'Yan Arewa ta na neman Magajin Buhari a 2023

Vanguard ta rahoto Abdul-Azeez Suleiman ya na cewa: “Shugaban kasa da jami’an tsaro suna ta fada mana suna yin wani abu game da sha’anin tsaro.”

“… amma yanzu duka mutanen Arewa sun gane cewa an yi watsi da yankinmu, an bar mu a hannun ‘yan ta’adda da suke cigaba da yi mana asara a Arewa.”

A cewar Mista Abdul-Azeez Suleiman, ana yi wa yankin Arewa illa ta fuskar siyasa da tattalin arzikin kasa da wadannan mutane na ta da ake hallaka wa.

“Uzurin nan da alkawuran karya sun isa haka.” Inji CNG.

KU KARANTA: Zan fada wa Buhari halin da ake ciki - Pantami

Jama’an da suke Arewa su kare kansu daga Boko Haram da Miyagu – Kungiyar CNG
Shugaban Najeriya Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Kungiyar take cewa “Duk ‘yan Arewa yanzu hankalin su ya tashi da karuwar rashin tsaro”, ganin yadda aka bar Bayin Allah a hannun miyagun ‘yan ta’adda.

CNG ta ce gwamnonin jihohi da shugaban kasa sun yi kasa a gwiwa a rantsuwarsu ta tsare jama’a.

Ta ce: “Halin da ake ciki yau a Arewa ya kai inda ya kai, don haka dole mu tashi tsaye, mu kare kanmu, mu nemi a yi wa gaba daya sha’anin tsaro garambawul.”

Dazu kun ji cewa an gano ainihin yawan Bayin Allah da aka kashe a mummunan harin da aka kai wa wasu manoman shinkafa a garin Zabarmari, a yankin Jere.

Wadanda Boko Haram din su ka yi wa yankan rago a jihar Borno sun haura mutum 110.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel