Baka san darajar da ka kara a idon masu caccakarka ba, Ndume ga Jonathan

Baka san darajar da ka kara a idon masu caccakarka ba, Ndume ga Jonathan

- Sanata Ali Ndume ya ce tsohon shugaban kasa, Jonathan ya kafa tarihin da ba za'a taba mantawa dashi ba

- Ndume wanda sai ranar Juma'a ya samu aka yi belinsa, bayan ya tsaya wa Maina amma aka neme shi aka rasa

- A cewarsa, a baya yana caccakar Jonathan, amma yanzu ya gane muhimmancinsa, kuma ya kara kima a idon jama'a

Ali Ndume, Sanatan Borno ta kudu, ya ce a baya yana caccakar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sanda yana kan mulki, amma yanzu yana kewarsa.

Kamar yadda aka gano Ndume ya fadi hakan a wani taron kaddamarwa da aka yi a Abuja. Ndume, wanda aka bada beli bayan ya kwashi kwanaki 5 a gidan gyaran hali ya ce Jonathan ya kafa tarihi a Najeriya.

An garkame Ndume a gidan gyaran hali bayan an nemi Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, wanda ya tsaya wa an rasa, The cable ta wallafa.

Baka san darajar da ka kara a idon masu caccakarka ba, Ndume ga Jonathan
Baka san darajar da ka kara a idon masu caccakarka ba, Ndume ga Jonathan. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

"Yadda Ubangiji yaso, haka yake kasancewa, saboda jiya ne aka sakoni daga gidan gyaran hali daren Juma'a, kila Ubangiji ya kaddara sai na zo wannan taron ne, in ba haka ba, da yanzu ina garkame a gidan gyaran hali," aka ji Ndume yana fadi.

KU KARANTA: Rashin adalcin PDP yasa na yi watsi da ita, Sanata Elisha Abbo

Ya kara da cewa, "Wajibi ne in fadi, kamar yadda mutane suke kallona a matsayin mutum mai taurin kai, ina da taurin kai. Wajibi ne in yi amfani da damar nan in yabi tsohon shugaban kasa, dama baka sanin darajar abu idan baka rasa shi ba.

"A kasar nan, ba a gane amfanin abu har sai an rasa. Muna godewa Ubangiji da ya raya ka har ka canja tsarin demokradiyyar da salon kasar nan.

"Baka san irin darajar da ka samu ba a idon wadanda basu sonka, da kuma wadanda basu je kusa da kai ba. Amma a baya ina daya daga cikin masu caccakarka.

"Ya so kara tsayawa takara, amma a yadda Najeriya take, al'amarin duk ya canja. Kamar yadda nace, ya kafa tarihi wanda ba za'a taba mantawa da shi ba a kasar nan."

KU KARANTA: Mugun dukan da 'yan sanda suka yi min yasa ni fitsari a wando, Budurwa

A wani labari na daban, wani mai fadi aji a jam'iyyar APC, Julius Ihonvbere, ya ce har yanzu shugaba Buhari bai nuna alamar goyon bayan Goodluck Jonathan ba a kan kara tsayawa takara.

Idan ba a manta ba, Legit.ng ta bayyana rahotonni sun nuna yadda APC take kokarin gamsar da Jonathan, tsohon shugaban kasan Najeriya, ya tsaya takara a 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng