An yi nadin manyan muhimman sarautu guda 7 a masarautar Katsina
- Masarautar Katsina ta yi kasaitaccen biki na nadin wasu sarautu guda bakwai
- Taron wanda aka gudanar a ranar Asabar, 29 ga watan Nuwamba, ya samu halartan manyan masu fada aji a kasar
- Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ne ya nada da sabbin hakiman
Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba, ya nada sabbin hakimai guda bakwai a wani kasaitacce biki da ya samu halartan manyan mutane a bangarori daban-daban.
Wadanda aka nada sune Sarkin Musawan Katsina, Alhaji Sagir Abdullahi Inde; Sarkin Yakin Katsina, Alhaji Bello Mamman Iffo; Matawallen Katsina, Kanal Abdulaziz Musa Yaradua mai ritaya.
Sai kuma mataimakin kwamanda Janar na rundunar NSCDC, Aminu Abdullah wanda aka nada wa sarautar Barayan Katsina.
KU KARANTA KUMA: An gano Ndume tare da Jonathan yan kwanaki bayan sakinsa daga kurkukun Kuje
Sauran wadanda aka nada sune, dan majalisar wakilai mai wakiltan Mani da Bindawa, Aminu Ashiru Mani, a matsayin Dokajin Katsina; Haruna Dalhatu kuma Sarkin Zango.
Har ila yau akwai mataimakin kwamishinan yan sanda, Suleiman Isah Ketare, wanda aka nada a matsayin Garkuwan Dokan Katsina.
An kuma nada Aminu Umar Sheme a matsayin Wazirin Zangunan Katsina.
Taron wanda ya gudana a harabar fadar sarkin ya ja hankalin manyan mutane irinsu gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari da takwaransa na jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad.
KU KARANTA KUMA: Da sauran rina a kaba: ASUU ta yi karin haske a kan rahotannin janye yajin aiki
Hakazalika ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila duk sun hallara, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A wani labarin, Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatad da shugaban kwamitin masu zaben sarkin Zazzau, Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu, Sahara Reporters ta ruwaito.
Hakazalika ta gargadi Iyan Zazzau, Aminu da sauran mambobin kwamitin zaben sarkin uku su canza lauyansu zuwa lauyan gwamnati a karar da suka shigar kotu, kan nadin Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng