An gano Ndume tare da Jonathan yan kwanaki bayan sakinsa daga kurkukun Kuje

An gano Ndume tare da Jonathan yan kwanaki bayan sakinsa daga kurkukun Kuje

- Sanata Ali Mohammed Ndume ya samu yanci a yanzu bayan shafe yan kwanaki a tsare

- An tsare Ndume a gidan gyara hali yan kwanaki da suka shige lokacin da wanda ya tsayawa a matsayin jingina ya tsere

- Tuni sanatan ya koma harkokin gabansa yayinda aka gano shi a wani taro a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba

An gano Sanata Mohammed Ali Ndume a wajen wani taro a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba, a Abuja yan kwanaki bayan sakinsa daga gidan gyara hali.

Taron ya samu halartan tsohon Shugaban kasar Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan, wanda ya wallafa hotunan taron a shafinsa na soshiyal midiya.

Har ila yau a cikin hoton da Jonathan ya wallafa an gano Bala Ngilari, tsohon gwamnan jihar Adamawa.

An gano Ndume tare da Jonathan yan kwanaki bayan sakinsa daga kurkukun Kuje
An gano Ndume tare da Jonathan yan kwanaki bayan sakinsa daga kurkukun Kuje Hoto: @GEJonathan
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: PDP ta kafa kwamitin mutane 6 domin fara zawarcin gwamnonin APC

Ndume ya shafe yan kwanaki a kurkukun Kuje bayan Justis Okon Abang ya yi umurnin cewa a tsare sanatan haifaffen Borno kan rashin gabatar da Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban fansho.

Ndume wanda ya kasance shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji, ya tsayawa Maina a matsayin jingina a lokacin shari’arsa.

KU KARANTA KUMA: Kisan manoma 44 a Borno: Gwamnatinmu ta yi iyakar kokarinta, Buhari

Sai dai kamun Sanata Ndume, ya haifar da cece-kuce daga kungiyoyin arewacin kasar wadanda suka ce lallai kamun nasa ba adalci bane.

Daya daga cikin kungiyoyin, Arewa Youth Consultative Forum (AYCF), ta yi Allah-wadai da abunda ta bayyana a matsayin tsare sanatan ba bisa ka’ida ba saboda ya ki gabatar da Maina.

A baya mun kuma ji cewa babban kotun tarayya dake Abuja ta baiwa Sanata mai wakiltan Borno ta kudu, Ali Ndume, wanda aka tsare a kurkuku tun ranar Litinin beli.

Alkali Okon Abang a hukuncin da ya yanke ranar Juma'a ya ce ya yanke shawaran baiwa Sanata Ndume beli ne saboda tarihinsa na halayya mai kyau, amma ba dan uzurorin da ya gabatar ba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel