2023: Jigon APC ya bayyana matsayar Buhari a kan takarar Goodluck Jonathan

2023: Jigon APC ya bayyana matsayar Buhari a kan takarar Goodluck Jonathan

- Alamu sun nuna cewa Buhari ba zai mara wa Jonathan baya ba a kan tsayawa takara a 2023, cewar Julius Ihonvbere

- A cewar dan majalisar kuma ginshikin Jam'iyyar APC, duk mai lura da yanayin Buhari zai fahimci hakan

- Duk da dai an ga yadda wasu gwannonin jam'iyyar APC suka ziyarci Jonathan ranar zagayowar haihuwarsa

Wani mai fadi aji a jam'iyyar APC, Julius Ihonvbere, ya ce har yanzu shugaba Buhari bai nuna alamar goyon bayan Goodluck Jonathan ba a kan kara tsayawa takara.

Idan ba a manta ba, Legit.ng ta bayyana rahotonni sun nuna yadda APC take kokarin gamsar da Jonathan, tsohon shugaban kasan Najeriya, ya tsaya takara a 2023.

Duk da an samu rahotonni a kan yadda yake zuwa fadar shugaban kasa akai-akai, Jonathan bai bayyana ra'ayinsa ba a kan tsayawa takarar shugabancin kasa ba a 2023 har yanzu.

2023: Jigon APC ya bayyana matsayar Buhari a kan takarar Goodluck Jonathan
2023: Jigon APC ya bayyana matsayar Buhari a kan takarar Goodluck Jonathan. Hoto daga Goodluck Jonathan, Muhammadu Buhari
Source: Facebook

KU KARANTA: Girgizar zukata: Hotunan masoya da suka gano mahaifinsu daya ana saura kwanaki aurensu

Cece-kuce sun kara yawa bayan wasu gwamnonin APC sun kai wa Jonathan ziyara don taya shi murnar cikar shi shekaru 63.

Ihonvbere, mai wakilar mazabar Owan ta yamma maso kudu a majalisar wakilai ya sanar da Vanguard cewa ba ya tunanin Buhari zai mara wa Jonathan baya don ya maye gurbinsa.

Dan majalisar ya ce: "Idan dai wannan Buharin ne da muka sani, duk mai lura zai gane cewa babu alamar zai bari Jonathan ya gaje shi.

"Sannan ya kamata Jonathan ya tuna cewa a lokacinsa akwai abubuwa da dama da bai dakatar ba a lokacin mulkinsa, kuma ya kamata a ce ya dakatar."

Ya shawarci tsohon shugaban kasar da kada yayi gaggawar daukar mataki a kan tsayawa takara a 2023, don kada ya zubar da ragowar mutuncinsa bayan ya amince da kayen da aka yi masa a 2015.

KU KARANTA: Mugun dukan da 'yan sanda suka yi min yasa ni fitsari a wando, Budurwa

A wani labari na daban, Sanata Ishaku Abbo, mai wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar dattawa, ya bayyana canja shekarsa daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya ce ya bar jam'iyyar PDP ne don kowa ya san shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel