Mugun dukan da 'yan sanda suka yi min yasa ni fitsari a wando, Budurwa

Mugun dukan da 'yan sanda suka yi min yasa ni fitsari a wando, Budurwa

- Da 'yan sanda suka fara dukana kamar bakuwar karya, sai da na fita hayyacina na tsula fitsari, cewar wata Felicia

- A cewarta, wasu 'yan sanda da ke Surulere, jihar Legas, sun azabtar da ita matuka don ta sha duka da naushi

- Ta ce ta daga waya tana daukar bidiyon zanga-zangar EndSARS, hakan ne ya fusata 'yan sanda suka hau dukanta

Felicia Okpara, ta ce 'yan sanda sun cutar da ita saboda ta daga waya tana daukar bidiyon zanga-zangar EndSARS da matasa suka yi a Surulere da ke jihar Legas.

A ranar Juma'ar da ta gabata, Okpara ta kai korafinta gaban kwamitin bincike na cin zarafin 'yan sanda na jihar Legas, Channels TV ta wallafa.

A cewar Okpara, ta gama wata tattaunawa kenan, sai ta dauki hanyar tafiya gida, da ta ga ana zanga-zangar, sai ta shiga.

Bakin dukan da 'yan sanda suka yi min yasa na fitsari a wando, Budurwa
Bakin dukan da 'yan sanda suka yi min yasa na fitsari a wando, Budurwa. Hoto daga @ChannelsTV
Source: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon mugun dukan da sojoji suka yi wa budurwa a kan kin gaiashesu ya janyo cece-kuce

Bayan nan ne sai taji harbi, kowa ya fara gudun neman tsira. Kamar yadda tace, ta gudu gefen wani ofishin 'yan sanda, sai ta ciro wayarta ta fara daukar bidiyo, sai ga wani dan sanda ya gabato ta. Ya fara umartar ta da ta daina daukar bidiyon, ita kuma ta ki dainawa.

Sai ya ciro bindiga ya ja ta cikin ofishin 'yan sandan tare da wata mata.

Su na isa ciki, sai 'yan sanda har da mata suka hau dukansu suna naushinsu. A cewarta, da taji shigar duka har fitsari ya kubuce mata.

"Da naji azaba, sai wayata ta fadi kasa, daya daga cikin 'yan sandan ya taka wayar saboda a tunaninsa zan sanya bidiyon abinda na dauka a yanar gizo ne," a cewarta.

KU KARANTA: Gwamna ya umarci kwamishinansa da ya tafi jinyar tsohon shugaban majalisar dattawa a Landan

"Tun muna bakin ofishin, 'yan sanda suka fara tururuwar fitowa suna dukanmu suna janmu cikin ofishin suna naushinmu," Okpara tana maganar tana zubar da hawaye.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya fatattaki wasu jami'an kula da kananun hukumomi 2. Dama ya fara fatattakar ma'aikata tun bayan ya canja sheka.

Ya kori Okorie Daniel na Ivo DC da Fabian Ivoke na Echiele DC, saboda kin amincewa da wata takarda da suke tunanin za ta bata sunan tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel