Girgizar zukata: Hotunan masoya da suka gano mahaifinsu daya ana saura kwanaki aurensu

Girgizar zukata: Hotunan masoya da suka gano mahaifinsu daya ana saura kwanaki aurensu

- Sai da na gabatar da ita, mahaifina ya tabbatar min da cewa kanwata ce, cewar Njoroge

- Wani saurayi dan kasar Kenya yana shirin angwancewa da Wanjiku ya gano kanwarsa ce

- Mahaifinsa ya tabbatar masa da cewa Wanjiku diyar kishiyar mahaifiyarsa ce, dole aure ya fasu

Wasu masoya 2 'yan kasar Kenya sun gano cewa yaya da kanwa suke, ana saura 'yan kwanaki kadan shagalin bikin aurensu.

An umarci John Njoroge ya dakata da shirye-shiryen aurensa da Rose Wanjiku, (ba sunayensu na asali ba), bayan ya turo magabatansa, The Nation ta wallafa.

Al'amarin ya daga wa Njoroge hankali, bayan ya gano cewa ubansu daya da Wanjiku domin diya ce ita ga kishiyar mahaifiyarsa.

Girgizar zukata: Hotunan masoya da suka gano mahaifinsu daya ana saura kwanaki aurensu
Girgizar zukata: Hotunan masoya da suka gano mahaifinsu daya ana saura kwanaki aurensu. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Kamar yadda ya bayyana wa gidan talabijin din Kameme, "Bayan da na gabatar da ita ga iyayena, mahaifina ya shaida min cewa ni yayanta ne, diya ce ita ga kishiyar mahaifiya ta."

Girgizar zukata: Hotunan masoya da suka gano mahaifinsu daya ana saura kwanaki aurensu
Girgizar zukata: Hotunan masoya da suka gano mahaifinsu daya ana saura kwanaki aurensu. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Duba tsoffin hotunan Gwamna Ganduje da matarsa yayin da suke shan amarci

Njoroge ya fara soyayya da budurwar sa ne bayan ta siya takalmi a wurinsa, wanda ya kai mata har gida domin neman yada manufarsa.

Girgizar zukata: Hotunan masoya da suka gano mahaifinsu daya ana saura kwanaki aurensu
Girgizar zukata: Hotunan masoya da suka gano mahaifinsu daya ana saura kwanaki aurensu. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Wanjiku ta bayyana tsoronta a kan fara wata soyayyar da wani. A cewarta, "Ina tsoron kara fadawa soyayya da wani, saboda kada in kara gane dan uwana ne."

KU KARANTA: Bidiyon amarya tana cashewa cike da gwaninta a liyafar bikinta ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, wata budurwa mai suna Olaide Oluwo, tana bukatar a yi mata adalci bayan wani sojan Najeriya da ke Sangotedo, jihar Legas ya ci zarafinta a ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda ta wallafa bidiyonta a kafar sada zumuntar zamani, wanda tace ya ci zarafinta ne saboda ba ta gaishesu ba.

"Wannan al'amarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yamma. Ban yi musu komai ba. Ko kallonsu ban yi ba, sai ga daya daga cikinsu da bulala, ya fara bugu na kamar jaka! Ina cikin tafiya ya zage ni kuma ya bi ni yana duka da bulala."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng