Daga komawa APC, gwamna Umahi ya sallami hadimansa 4

Daga komawa APC, gwamna Umahi ya sallami hadimansa 4

- Gwamnan Ebonyi ya sake rabuwa da wasu hadimansa bayan komawa APC

- Ya shahara da sallaman hadimansa idan ya fahimci ba sa aikinsu yadda ya bukata

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya sallami hadimansa hudu kan zargin yiwa aikin da ya basu rikon sakainar kashi.

Sakataren gwamnan jihar, Kenneth Ugbala, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki kuma kamfanin dillanci labarai, NAN, ta ruwaito ranar Asabar.

Wadanda aka sallame sun hada da Cletus Ogbonna, John Osi, Tochukwu Ali da Olachi Arua.

"Ana umurtan dukkan wadanda aka sallama su mika dukiyoyin gwamnati dake hannunsu ga SSG nan da ranar Litinin 23 ga Nuwamba," jawabin yace.

Gwamnan, wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ranar 20 ga Nuwamba, ya sallami hadimansa da dama da suka zo daga karamar hukumar Ohaukwu.

Wadanda sharan ya shafa sun hada da sukkan jagororin kananan hukumomi, hadimai, manyan hadimai, dss.

KU KARANTA: INEC ta haramtawa APC musharaka a zaben maye gurbin kujeran Sanata da za'a yi

Daga komawa APC, gwamna Umahi ya sallami hadimansa 4
Daga komawa APC, gwamna Umahi ya sallami hadimansa 4
Asali: Twitter

A jiya kuwa, Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana cewa gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta fi alhairi fiye da shekaru 16 da gwamnatin Peoples Democratic Party (PDP).

Umahi ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma'a a hirar da yayi a shirin Politics Today na tashar Channels TV.

DUBA NAN: Yan bindiga sun budewa mutane wuta kusa da tashar jirgin kasan Kaduna

"Idan ka kwatanta, ina ganin yan shekarun gwamnatin APC sun fi na tsohuwar jam'iyyata. Babu wani mai kama karya kan lamuran jam'iyyar," Umahi yace.

Umahi ya ce jihar Ebonyi ta amfana da APC cikin shekaru 5 da suka gabata fiye da yadda ta amfana da PDP cikin shekaru 16 da tayi mulki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel