An dakatar da komawa kan sabon tsarin shan wutar lantarki sai wani mako - Minista

An dakatar da komawa kan sabon tsarin shan wutar lantarki sai wani mako - Minista

- An yi zama tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago a Aso Villa

- Ministan kwadago ya ce an dakatar da karin kudin wuta sai nan da wani mako

- Haka zalika an samu raguwar farashin shan wuta a kan karin da aka yi kwanaki

Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar12 ga watan Oktoba, 2020, cewa an dakatar da maganar dabbaka sabon farashin shan wutar lantarki.

Gwamnatin tarayya ta bada umarnin kara wa’adin mako guda, kafin karin da aka yi ya koma aiki.

A ranar 28 ga watan Satumba, gwamnatin kasar ta ce ta dakatar da amfani da sabon farashin da aka kawo, bayan ta zauna da kungiyoyin kwadago.

Yanzu haka an sake kara wa’adin wannan sarari a daidai lokacin da ake shirin komawa sabon karin da aka yi wa wasu daga cikin masu shan wuta.

KU KARANTA: An yi daidai da aka kara kudin wuta Inji Sanusi Lamido Sanusi

Gwamnatin tarayya ta cin ma wannan matsaya ne a sakamakon zaman da aka yi tsakanin bangarorin gwamnatin tarayya da kuma TUC da NLC.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya jagoranci wannan zama a fadar Aso Villa.

A sakamakon wannan zama, an yarda cewa za a raba na’urorin awon wuta miliyan shida a Najeriya, wannan zai yi maganin karancin na’urorin.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, za a raba na’urorin ne kyauta ba tare da jama’a sun biya sisin kobo ba, CBN za ta fito da kudin da za ayi wannan aikin.

KU KARANTA: Wutar lantarki: Talaka sai hakuri a Najeriya - Kyari

An dakatar da komawa kan sabon tsarin shan wutar lantarki sai wani mako - Minista
Chris Ngige Hoto: Elobmah
Asali: UGC

Jaridar ta ce ana sa ran cewa za a fara wannan aiki na rabon na’urorin a makon nan da aka shiga.

Haka zalika an tsaida magana cewa za a saye na’urorin ne daga hannun kamfanonin gida kamar yadda Ministan kwadago, Chris Ngige ya bayyana.

Dr. Chris Ngige ya tabbatar da cewa an yarda a rage kudin shan wuta ga wadanda ke sahun Band A, B, da C da kaso 10%, 10.5% da kuma 31%.

Kwanaki ku ka ji cewa Muhammadu Buhari ya amince da bukatar sabon tsarin kudin wutar lantarki na NESI (Nigerian Electricity Supply Industry).

Jaridar TheCable ta ce sabon tsarin karin wutar lantarkin ba zai shafi talakawa tubus ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng