'Yan Najeriya za su yi alfahari da Buhari a kan kokarinsa a fannin wutar lantarki - Saleh Mamman

'Yan Najeriya za su yi alfahari da Buhari a kan kokarinsa a fannin wutar lantarki - Saleh Mamman

- Ministan wutar lantarki na Najeriya, Saleh Mamman ya ce nan babu dadewa 'yan Najeriya za su yi alfahari da Buhari

- Ya ce shugaban kasar ya yi matukar kokari a fannin wutar lantarkin kasar nan kuma babu jimawa za a ga hakan

- Ya sanar da hakan ne a shafinsa na Twitter a wallafar da yayi a ranar Laraba a kan tarin cigaban da aka samu a fannin wutar lantarki

Saleh Mamman, ministan wutar lantarki ya ce nan ba da dadewa ba, yan Najeriya zasu yi alfahari da yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gyara fannin wuta.

A ranar Laraba, ministan ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda yace, wannan mulkin ya samar da cigaba mai tarin yawa a ma'aikatar wutar lantarki.

Mamman ya ce wannan mulkin a shirye yake da yayi gyara a bangarorin da ya lalace.

"Nan ba da dadewa ba, 'yan Najeriya zasu waiwaya baya cikin alfahari, su ce lallai mulkin Shugaba Buhari yayi gyara mai tarin yawa a fannin wutar lantarki. Yanzu haka kokarin da mukeyi kenan!", a cewar Mamman.

Ya kara da cewa, "yanzu haka mun samu cigaba sosai, kuma muna sanar da 'yan Najeriya abinda ake ciki."

A shekarar 2019, shugaban kasa yasa hannu akan wata yarjejeniya ta wutar lantarki da Siemens AG, wani kamfani dake kasar Jamus, wadanda zasu dinga bayar da megawatts 7000 na wuta a shekarar 2021.

A watan Mayu, Buhari ya aminta da bada kudi a kashi na farko don yarjejeniyar wutar lantarkin Siemens.

Wata rana, 'yan Najeriya za su yi godiya ga Buhari a kan kokarinsa a fannin wutar lantarki - Saleh Mamman
Wata rana, 'yan Najeriya za su yi godiya ga Buhari a kan kokarinsa a fannin wutar lantarki - Saleh Mamman. Hoto daga @EngrSMamman
Asali: Twitter

KU KARANTA: Damfara: Shugaban KAROTA zai gurfana a gaban kotu

KU KARANTA: Harin tawagar Zulum: Rundunar soji na goyon bayan mayar da 'yan gudun hijira gida

A wani labari na daban, Kkungiyar Igbo for President Solidarity Congress (IPSC), wata kungiya ce a kudu maso yammacin Najeriya, ta tabbatar da bada hadin kai dari bisa dari akan shugabancin dan kudu maso gabas a shekarar 2023.

Ta ce yin hakan ne kadai zai kawo hadin kai a Najeriya. Shugaban kungiyar, Dr Olukayode OshinAriyo ne yayi wannan kiran a ranar Talata, 29 ga watan Satumba a Ibadan, jihar Oyo.

IPSC ta ce kamar yadda kundin tsarin mulkin 1999 ya nuna, kudu maso gabas suna da damar rike kujerar shugabancin kasar Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel