Alkali ya sa ranar sauraron shari’ar karar wadanda suka zagi Manzon Allah

Alkali ya sa ranar sauraron shari’ar karar wadanda suka zagi Manzon Allah

- Alkali ya fara sauraron shari’ar wanda ake zargi da yi wa Annabi batanci

- Yahaya Aminu Sharif da Umar Faruk sun daukaka kara zuwa babban kotu

- Mai shari’a Nasiru Saminu ya ce zai sa ranar da za a yanke hukuncin karshe

Babban kotun daukaka kara da ke jihar Kano, ta tanadi lokacin da zata yanke hukunci game da karar da aka shigar na batanci ga Manzon Allah SAW.

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa Alkalin kotun ya fitar da ranar da zai zartar da hukuncin karan da ake gabansa na wani matashi, Yahaya Aminu Sharif.

Jaridar ta ce ana zargin wannan mutumi watau Yahaya Aminu Sharif da laifin yi wa Annabi Muhammad SAW batanci, har aka yi masa hukuncin kisa.

KU KARANTA: Kotu ta sa tsaro a shari'ar batanci ga Annabi a Kano

Haka zalika akwai wani Bawan Allah, Umar Faruk mai shekara 13 da babban kotun shari’ar ta zartar wa hukuncin daurin shekara 10 kwanakin baya.

Duka wadannan mutane biyu sun daukaka kara a babban kotun na jihar Kano, suna neman ayi fatali ko akalla a sassauta hukuncin da aka yanke masu.

Da aka fara zaman sauraron daukaka karar a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2020, Lauyan da ya tsaya wanda ake tuhuma ya roki a soke hukuncin baya.

Barista Kola Alapinni ya yi ikirarin ba a ba wadanda ake zargi damar kare kansu kamar yadda dokar kasa ta tanada ba.

Alkali ya sa ranar sauraron shari’ar karar wadanda suka zagi Manzon Allah
Ana zargin Yahaya Sharif Aminu da cin mutuncin Manzon Allah Hoto; www.withinnigeria.com
Source: UGC

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya yi magana game da halin da Najeriya ke ciki

Ita kuwa lauyar gwamnati, Barista Aisha Mahmud ta roki Alkali mai shari’a ya tabbatar da hukuncin kisa da daurin da aka yanke a kan wadannan mutanen.

Alkali mai shari’a Nasiru Saminu ya ce zai zartar da hukunci, kuma da zarar ya sa rana zai sanar da wadanda ake tuhuma da wadanda su ka shigar da karar.

A shari'ar Abdulrasheed Maina da EFCC, mun ji cewa Alkalin ya fara neman ‘Dan Majalisa na biyu da ya tsaya wajen bada beli, a dalilin arcewar Maina da 'Dansa.

Kotu ta fadawa ‘Dan Majalisar da ya cusa kansa a shari’ar ya bayyana ko kuma ya ji babu dadi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel