Ya tabbata Nigeria na cikin wani hali duba ga tsadar albasa, In ji Sarkin Musulmi

Ya tabbata Nigeria na cikin wani hali duba ga tsadar albasa, In ji Sarkin Musulmi

- Sultan na Sakkwato, Alhaji Abubakar Sa'ad III, ya koka a kan mawuyacin halin da kasar ke ciki a yanzu

- Sarkin Musulmin ya bayyana cewa tsadar albasa kadai da ake fama dashi a kasar nan ya isa nuni ga cewar tattalin arzikin kasar na cikin wani yanayi

- Ya kuma yi tsokaci a kan matsalar rashin tsaro da ke kara tabarbarewa a kulla-yaumin

Mai martaba sarkin Musulmi kuma Sultan na Sakkwato, Alhaji Abubakar Sa'ad III, ya yi tsokaci a kan matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki da Najeriya ke fama da su a yanzu haka.

Sultan, da yake jawabi a wajen taron majalisar shugabannin addinai ta kasa, ya bayyana cewa yadda albasa ta yi tsada ya tabbatar da girman wahalar tattalin arzikin da ake ciki a yanzu a Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wallafa Majalisar ƙoli ta harakokin addinin musulunci tayi a shafinta na Twitter.

Ya tabbata Nigeria na cikin wani hali duba ga tsadar albasa, In ji Sarkin Musulmi
Ya tabbata Nigeria na cikin wani hali duba ga tsadar albasa, In ji Sarkin Musulmi Hoto: @NSCIAng
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yakubu Gowon ya mayar da martani ga dan majalisar Birtaniya da ya zarge shi da sace rabin kudin CBN

Sarkin musulmin ya ce:

“Yadda albasa ta yi tsada a Najeriya a yau alamu ne da ke nuna mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a yanzu. Ba wai mun rasa shawarwari da maganin matsalolinmu bane. Abunda muka rasa shine tunanin manufofi.”

Har ila yau, Sultan ya yi Allah-wadai da yadda lamarin tsaro ke kara tabarbarewa a kasar musman a Arewacin kasar, yace a yanzu yan bindiga na cin karansu ba babbaka.

Cewa suna bi gida-gida suna garkuwa da mutane ba tare da shamaki ba.

KU KARANTA KUMA: Mutum ne mai mutunci, Shugaban bankin AfDB Adesina ya kare Gowon kan zargin sata

A wani labarin, manoman Najeriya a ranar Laraba sun yi Alla-wadai da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na sake bude iyakokin Najeriya na kasa.

Sun bayyana cewa bude iyakokin a yanzu da kayan abinci ke hauhawa abune mai hadarin gaskiya.

Sun ce kasashe makwabta da suka dogara kan Najeriya wajen samun kayan abinci zasu shigo kasar kuma hakan zai sa kayan abinci ya sake hauhawa, Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel