Batanci ga Annabi: An tsananta tsaro a kotun daukaka kara da ke Kano

Batanci ga Annabi: An tsananta tsaro a kotun daukaka kara da ke Kano

- Matakan tsaro sun kara tsauri a farfajiyar babbar kotun Kano a ranar Alhamis

- Kowa yana so ya ji yadda za ta kaya a kan shari'ar mazan nan 2 da suka yi batanci ga musulunci

- Dama an dage sauraron shari'ar ne daga watan Oktoba zuwa yau 26 saboda wasu manyan dalilai

Matakan tsaro sun tsananta a farfajiyar babbar kotun Kano a ranar Alhamis ana saura sa'o'i 2 a fara shari'a a kan wadanda suka yi batanci ga musulunci, Daily Trust ta wallafa.

Dama kotun ta sanya ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamban 2020 don sauraron kararraki 2 da aka daga saboda lauyoyi basu samu damar zuwa kotu ba a wancan zaman.

Kara 2 ne za a saurara na wani Yahaya Aminu Sharif mai shekaru 22, wanda babbar kotun musulunci ta yankewa hukuncin kisa, da wani Umar Faruk, mai shekaru 13, wanda aka yankewa hukuncin shekaru 10 a gidan yari.

Batanci ga Annabi: An tsanata tsaro a kotun daukaka kara da ke Kano
Batanci ga Annabi: An tsanata tsaro a kotun daukaka kara da ke Kano. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Taiwo Olowo: Basaraken da aka dade ba a yi mai arziki irinsa ba a Legas, yadda ya tara kudinsa

A zaman kotun na baya, wanda aka yi a watan Oktoba, ya kamata lauyoyin masu daukaka kara su taso tun daga jihar Legas, amma ba su samu damar isa kotun ba. Sai dai wani Zubairu Suleiman Usman ya sanar da kotu uzirinsu.

Usman ya sanar da kotu cewa sun kira shi inda suka bukaci ya sanar da kotu cewa ba za su samu damar zuwa ba, kuma suna bukatar kotu ta daga zaman kotun zuwa 26 zuwa 30 ga watan Nuwamba.

Lauyan masu kai kara, Antoni janar na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawal, ya ce su bi ta hanyar da ya dace, su rubuta takarda wacce za ta bayar da damar amincewar kotu don ta amince da lokacin da suka bukata.

KU KARANTA: Duba tsoffin hotunan Gwamna Ganduje da matarsa yayin da suke shan amarci

A shari'arshi, Alkali Nasiru Saminu, ya duba yadda masu zanga-zangar EndSARS suka rikita jihar Legas, da yanayin yadda shari'ar take da hatsari, ya amince uzirinsu. Kuma ya amince da uzurinsu, don haka ya dage shari'ar zuwa 26 ga watan Nuwamba don ya saurari shari'ar.

A wani labari na daban, majalisar tarayya ta umarci kwamitin sadarwa da ta gayyaci ministan sadarwa, Dr Ali Isa Pantami, don ta fahimtar dashi bukatar samar da mafita a kan tsaro ta ma'aikatarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel