Zargin satar N2bn: Kotu tana cigiyar Hon. ‘Dan Galadima da Faisal Maina
- Lauyan EFCC yana neman Kotu ta daure Sani Umar Dan-Galadima a kurkuku
- Sani Umar Dan-Galadima shi ne wanda ya tsaya wa Faisal Abdulrasheed Maina
- ‘Dan Majalisar yana cikin barazanar rasa N60m ko a garkame shi a gidan yari
Babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ya na neman ‘dan majalisa Sani Umar Dan-Galadima ya bayyana a shari’ar Alhaji Abdulrasheed Maina.
A ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, 2020, Alkali mai shari’a Okon Abang ya yanke hukunci cewa dole Sani Umar Dan-Galadima ya zo kotu gobe.
Okon Abang ya na son ganin Honarabul Sani Umar Dan-Galadima ne a ranar Laraba, idan bai yi hakan ba, zai bada umarnin jami’an tsaro su kama shi.
KU KARANTA: Maina: Kotu ta bukaci a tsare mata Maina a gidan yari
Bayan haka, dazu jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Alkalin ya bada umarnin a kamo masa yaron wanda ake tuhuma, Faisal Abdulrasheed Maina.
Hukumar EFCC ta dogara da sashe 354 (2) na dokar ACJA, ta nemi Alkali ya cigaba da shari’a a kan Faisal Maina ko da ba a ga fuskarsa a cikin kotu ba.
‘Dan-Galadima mai wakiltar mazabar Kauran Namoda, jihar Zamfara a karkashin jam’iyyar PDP ne tsaya wa Faisal Abdulrasheed Maina a gaban kuliya.
Idan ba haka ba, ‘dan siyasar zai iya rasa kudinsa Naira miliyan 60 a hannun gwamnatin tarayya.
KU KARRANTA: Ba ayi wa Ndume adalci ba - Kungiya
Lauyan EFCC, Barista M.S. Abubakar ya sanar da kotu cewa ba a ga keyar Faisal Maina da wanda ya tsaya masa ba, don haka ya nemi a soke belin da aka basu.
Abubakar ya na so a aika ‘dan majalisar zuwa gidan yari ko kuma ya hakura da kudin da ya bada.
A yau kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya kwana a gidan gyaran hali na Kuje, Abuja bisa umarnin babbar kotun tarayya dake Abuja a shari'ar Abdulrasheed Maina.
Sanatan ya ce zai daukaka kara akan hukunci da aka yanke masa yau domin ya samu 'yanci.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng