Ka fito da kanka don kare Ndume daga wannan tozarcin, dan uwan Maina ya roke shi
- Aliyu Maina, dan uwan tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, ya roki kawunsa a kan ya mika kansa ga yan sanda
- Maina na fuskantar shari’a a kan almubazaranci da kudaden fansho
- An tsare Sanata Aliyu Ndume wanda ya tsaya wa Maina a matsayin jingina a gidan maza, a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba
Kwanaki biyu bayan babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tsare sanata mai wakiltan Borno ta Kudu, Ali Ndume a gidan yari kan rashin gabatar da Abdulrasheed Maina a kotu, dan uwan tsohon Shugaban hukumar ta fansho, Aliyu Maina ya yi martani.
Aliyu ya bukaci kawun nasa a kan ya gabatar da kansa ga rundunar yan sanda.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Aliyu ya ce sake bayyanar Maina zai dakatar da tozarcin da Ndume ke fuskanta a idon duniya kafin lamarin ya tabarbare.
KU KARANTA KUMA: Hariji kuma matsafi: Kotu ta raba auren mijin da ke saduwa da matarsa tsawon awanni
Legit.ng ta tattaro cewa Aliyu, dan uwan Maina na kut-da-kut, ya ce sanata Ndume ya azabtu sosai a kan Maina.
Ya kara da cewa abun bakin ciki ne ganin cewa yana biyan bashi don kawai ya taimaki dan mazabarsa.
Aliyu ya yi kira ga Maina a kan ya taimaki halin da ake ciki, cewa tserewar na kara tabarbarar da shari’arsa ne, sannan cewa ya gabatar da kansa don a samu damar kawo karshen al’amarin.
Ya ce:
“Na yi magana da Sanata Ndume da wasu hadimansa lokuta da dama kuma na basu tabbacin cewa Maina zai gurfana a gaban kotu da zaran ya warke, amma abun bakin ciki, ya ki aikata hakan. Ban sanya idanu a kansa ba tsawon watanni uku yanzu domin yana gudun kowa.”
KU KARANTA KUMA: Hukumar kurkukun Kuje ta saka takunkumi, ta hana 'yan majalisa ganin Ndume
A gefe guda, Kungiyar matasan Arewa , ta yi Allah wadai da tsare sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, bisa yadda ya kasa gabatar da Abdulrasheed Maina.
Maina ya gudu daga beli akan almundahanar kudi Naira biliyan 2 kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng