Maina: Ƙungiyar matasan arewa ta yi tir da tsare Ndume

Maina: Ƙungiyar matasan arewa ta yi tir da tsare Ndume

- Kungiyar matasan arewa ta Arewa Youth Consultative Forum ta bayyana ra'ayinta kan tsare Sanata Ali Ndume na JIhar Borno

- Babbar Kotun Tarayya a Abuja ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, ta bada umarnin tsare Ndume bayan kasa gabatar da Abdulrasheed Maina

- Kungiyar matasan arewan ta ce tayi mamakin yadda kotun ta bar Sanata Abaribe ya tafi bayan ya kasa gabatar da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu a gaban kotu

Kungiyar tuntuba ta matasan Arewa (AYCF), ta yi Allah wadai da tsare sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, bisa yadda ya kasa gabatar da tsohon Shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina.

Maina ya gudu daga beli akan almundahanar kudi Naira biliyan 2 kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Maina: Ƙungiyar matasan arewa sunyi Allah - wadai da tsare Ndume
Maina: Ƙungiyar matasan arewa sunyi Allah - wadai da tsare Ndume
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

Legit.ng ta ruwaito kungiyar ta bada wata sanarwa ta bakin shugaban ta, Yerima Shettima, wanda ya ce kungiyar ta ce tsare Ndume saboda guduwar Maina daga beli, a matsayin rashin adalci.

AYCF ta ce duk da bata karyata ko Maina ya aikata laifin da ake zargi ko a'a, ta ce bai kamata a saki Abaribe wanda ya tsayawa ɗan tawaye Nnamdi Kanu ya na yawo a matsayin mai yanci.

Sanarwar ta ce:

"Ba mu gane dalilin da yasa, Sanata Abaribe, wanda ya tsayawa shugaban Biafra wanda aka bayyana al'amuran a matsayin ayyukan ta'addanci (kuma har yanzu suna gudana) kuma an gaza hukunta shi.

KU KARANTA: A haramta wa yaran masu riƙe da muƙaman siyasa zuwa karatu ƙasashen waje, in ji ASUU

"Don tabbatar da daidaito da adalci, ya kamata a kama Abaribe kuma a tsare shi a gidan yari shima, har sai Nnamdi Kanu ya gabatar da kan sa. Da Ndume da Abaribe duk sanatocin Najeriya ne, saboda Abaribe bai fi Ndume ba. Duk kansu dokar kasa da kuri'un jama'ar yankin su ne suka kaisu matakin."

Kungiyar ta ce ta na da hakkin nuna cewa kowane ɗan kasa ɗaya suke kuma ba wanda yafi wani a Najeriya, kuma lamarin Ndume, Maina har yanzu zargin sa ake kuma ba wata kotu da ta yanke hukunci.

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel