Gwamnonin kudu maso kudu sun gabatar da wasu manyan bukatu 5 a gaban Buhari

Gwamnonin kudu maso kudu sun gabatar da wasu manyan bukatu 5 a gaban Buhari

- An gudanar da taro tsakanin gwamnoni da sauran masu fada aji a yankin kudu maso kudu da tawagar gwamnatin tarayya

- A yayin taron, jiga-jigan yankin kudancin kasar sun gabatarwa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu muhimman bukatu biyar

- Farfesa Ibrahim Gambari, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa ne ya jagoranci tawagar ta gwamnatin tarayya zuwa taron wanda aka yi a Port Harcourt

Gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki daga yankin kudu maso kudu sun gana da wata tawaga daga gwamnatin tarayya a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, a Port Harcourt, jihar Rivers.

Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Farfesa Agboola Ibrahim Gambari, ne ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayyar zuwa wajen ganawar.

An gudanar da taron ne domin magance sakamakon zanga-zangar EndSARS da sauran manyan lamura da suka addabi yankin.

Gwamnonin kudu maso kudu sun gabatar da wasu manyan bukatu 5 a gaban Buhari
Gwamnonin kudu maso kudu sun gabatar da wasu manyan bukatu 5 a gaban Buhari Hoto: @IAOkowa
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Hotunan kafin auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi da amaryarsa

Shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso kudu kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya gabatar da wasu muhimman bukata a gaban tawagar a madadin yankin.

Legit.ng ta lissafo jerin bukatun da yankin ta gabatar.

1. Sauya fasalin lamura, tsarin gwamnati na gaskiya da mika iko ga gwamnatocin kasa

2. Mayar da hedkwatar dukkanin manyan kamfanonin mai zuwa kudu maso kudu

3. Samar da rundunar yan sanda ta jiha

4. Kammala hanyoyin gabas maso yamma da dukkanin sauran hanyoyin tarayya a yankin

5. Farfado da manyan tashoshin ruwa na yankin a Port Harcourt, Calabar da Warri.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Niger za ta yanke albashin ma’aikata da 50% daga Disamba

A wani labari, Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya shiga cikin ‘yan siyasar da su ke tofa albarkacin bakinsu game da zabe mai zuwa na 2023, tun yanzu.

Mai girma gwamna Hope Uzodimma ya ce da lalama Ibo za su karbi mulkin Najeriya, ja-kunne cewa barazana da neman tada rigima ba za suyi aiki ba.

Gwamnan ya bayyana wannan ne a lokacin da aka kaddamar masa da sabon ‘dan takarar shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, George Obiozor.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng