Hotunan kafin auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi da amaryarsa

Hotunan kafin auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi da amaryarsa

- Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Nuhu Abdullahi na shirin angwancewa

- Za a kulla aure tsakanin Nuhu da amaryarsa Jamila Abdulnasir a ranar Juma’a, 4 ga watan Disamba, a jihar Kano

- Jarumin da kansa ya wallafa hotunan kafin aurensu a shafinsa na Instagram

Shahararren jarumin nan na Kannywood wanda tauraronsa ke kan haskawa a masana’antar shirya fina-finan ta Hausa, Nuhu Abdullahi na shirin angwancewa.

Za a daura auren Nuhu tare da amaryarsa Jamila Abdulnasir a ranar Juma’a, 4 ga watan Disamba, a jihar Kano.

Tuni dai manyan jaruman masana’antar da shi kansa angon suka fara wallafe-wallafen hotunan kafin auren masoyan biyu.

Hotunan kafin auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi da amaryarsa
Hotunan kafin auren jarumin Kannywood, Nuhu Abdullahi da amaryarsa Hoto: nuhuabdullahi
Asali: Instagram

A hotunankafin auren nasu wanda Legit.ng ta gano a shafin jarumin na nuhuabdullahi a Instagram, an gano masoyan biyu sanye da kayayyaki na alfarma da kamala.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Niger za ta yanke albashin ma’aikata da 50% daga Disamba

A cikin daya daga cikin hotunan, amaryar ta kasance sanye da atamfa launin ruwan kasa da launin ruwan gwal yayinda shi kuma angon ya saka dinkin babbar riga launin ruwan kasa shima.

A wani hoton kuma, angon ya saka farin shadda dinkin babban riga inda ita kuma sahibar tasa ta sanya dinkin doguwar riga launin ruwan hoda. Sun kuma rike junansu a hoton cike da shauki.

Jarumin ya kara shahara sakamakon wani shiri mai suna Labarina da masana’antar ke haskawa a yanzu wanda ya dauki hankalin ma’abota kallon fina-finan Hausa.

KU KARANTA KUMA: Taiwo Olowo: Basaraken da aka dade ba a yi mai arziki irinsa ba a Legas, yadda ya tara kudinsa

Ga hotunan da ya wallafa a shafinsa na Instagram a kasa

Ga katin gayyata zuwa wurin daurin auren:

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umarnin a sauya wa gidan ajiye naman jeji (gidan Zoo) matsuguni daga birnin Kano saboda matsarsa da jama'a suka yi.

Kwamishinan Al'adu da harkokin buɗe ido, Ibrahim Ahmad, shine ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Ya ce dabbobin, yanzu, a takure su ke a matsunguninsu saboda ko kadan basa son hayaniyar mutane.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng