Gwamnatin jihar Niger za ta yanke albashin ma’aikata da 50% daga Disamba

Gwamnatin jihar Niger za ta yanke albashin ma’aikata da 50% daga Disamba

- Gwamnatin jihar Niger na shirin yanke albashin ma’aikatan gwamnati da 50%

- Gwamnatin ta bayyana ragin da ta samu a kudaden shiga da gwamnatin tarayya ke bata a matsayin dalilinta na aikata hakan

- Sai dai kuma, kungiyar kwadago ta jihar ta ce za ta turje a kan duk wani shiri na zabtare albashin ma’aikata

Wani rahoton jaridar The Sun ya nuna cewa gwamnatin jihar Niger ta kammala shirye-shirye don yanke albashin ma’aikata a jihar da kaso 50 cikin dari domin ta lallabawa yayinda Najeriya ke gwagwarmaya da koma bayan tattalin arziki.

A cewar jaridar, gwamnatin jihar ta fada ma manyan jami’ai na kungiyar kwadago a wani taro a ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba, cewa ba za ta iya ci gaba da biyan kaso 100 na albashin ma’aikata ba daga watan Disamban 2020.

An tattaro cewa taron ya samu halartan dukkanin mambobin majalisar zartarwa ta jihar illa Gwamna Alhaji Abubakar Bello da mataimakinsa Alhaji Ahmed Mohammed Ketso.

Gwamnatin jihar Niger za ta yanke albashin ma’aikata da 50% daga Disamba
Gwamnatin jihar Niger za ta yanke albashin ma’aikata da 50% daga Disamba Hoto: @abusbello
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Kotu ta umurci ɗan majalisar tarayya ya gurfanar da ɗan Maina nan da kwanaki 9

Babban akawu na jihar, Alhaji Abdullahi Saidu ne ya sanarwa da shugabannin kungiyar kwadago halin da ake ciki.

Dalilin shirin yanke albashin

An tattaro cewa babban akawun ya yi bayanin cewa akwai ragowa sosai a kudaden da jihar ke samu daga asusun gwamnatin tarayya da kudaden shiga.

Sai dai, gwamnatin jihar ta yi alkawarin biyan ma’aikata kaso 50 da aka yi masu ragi da zaran tattalin arziki ya inganta.

Shugabannin kungiyar kwadago sun yi martani

A nasu martanin, kungiyar kwadago a jihar sun sha alwashin nuna turjiya a kan shirin yanke albashin ma’aikatan.

Basu amince da bayanin gwamnatin jihar da alkawarin biyan ragin da aka yi daga albashin daga baya ba.

KU KARANTA KUMA: Lauya ya yi watsi da Abdulrasheed Maina, yana neman janyewa daga shari’arsa

Legit.ng ta tattaro cewa ana sanya ran jami’an NLC da TUC za su gana a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, inda za su yanke hukuncin karshe kan matakin gaba da za a dauka.

A wani labarin, a kalla malaman makarantun firamare da na sakandare 4,250 gwamnatin jihar Katsina ta horar tsakanin 2015 zuwa yanzu.

Duk da haka, S-Power tana kara horar da malamai 7,000 don bunkasa ilimi a jihar, Channels Tv ta wallafa.

Gwamna Aminu Masari ya sanar da hakan a wani taro na bunkasa ilimi a jihar Katsina na 2020, wanda aka yi a ofishin kananan hukumomi da ke Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng