Wata sabuwa: Kotu ta umurci ɗan majalisar tarayya ya gurfanar da ɗan Maina nan da kwanaki 9
- Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba dan majalisar wakilai, Umar Sani Dan Galadima wa’adin kwanaki tara ya gabatar da Faisal Maina a gabanta
- Dan majalisar mai wakiltan mazabar Kaura Namoda na jihar Zamfara dai shine ya tsaya har aka bayar da belin wanda ake karan
- Justis Okon Abang ya ce idan har hakan bai samu ba toh Dan Galadima zai biya naira miliyan 60 da ke yarjejeniyar bayar da belin ko kuma a tura shi gidan maza
Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta ba dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Kaura Namoda na jihar Zamfara, Umar Sani Dan Galadima zuwa ranar 4 ga watan Disamba, ya gabatar da Faisal, dan Abdulrasheed Maina wanda ya gudu bayan beli.
An gurfanar da Faisal a gaban kotu kan laifukan da suka shafi zambar kudade.
An bayar da belinsa a watan Disamban 2019, inda Dan Galadima ya tsaya masa a matsayin jingina bayan ya sanya hannu a yarjejeniyar naira miliyan 60, The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Lauya ya yi watsi da Abdulrasheed Maina, yana neman janyewa daga shari’arsa
Justis Okon Abang, da yake zartar da hukunci a ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba, ya umurci Dan Galadima, wanda ya halarci zaman kotun, da ya gabatar da Faisal a ranar 4 ga watan Disamba.
Ko a kwace masa naira miliyan 60 da yayi alkawari a yayinda yake karban belin Faisal, ko kuma a tura shi gidan yari har sai ya gabatar da wanda ake kara.
A wani labarin, babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, za ta saurari bukatar neman bayar da belin sanata mai wakiltan Borno ta Kudu, Ali Ndume.
An tsare Ndume a gidan yari tun ranar Litinin, kan tsayawa tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, da yayi, inda shi kuma ya tsere.
KU KARANTA KUMA: Ka fito da kanka don kare Ndume daga wannan tozarcin, dan uwan Maina ya roke shi
Maina na fuskantar tuhume-tuhume na zambar kudade har naira biliyan biyu kafin aka bayar da belinsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng