Lauya ya yi watsi da Abdulrasheed Maina, yana neman janyewa daga shari’arsa

Lauya ya yi watsi da Abdulrasheed Maina, yana neman janyewa daga shari’arsa

- Wani lauya a cikin tawagar lauyoyin da ke kare tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, ya yasar da ubangidan nasa

- Lauyan mai suna Adeola Adedipe wanda ke wakiltan kamfanin Maina, Common Input Property and Investment Limited, ya nemi janyewa daga shari'ar

- Sai dai alkalin kotun, mai shari'a Okong Abang ya ce takardar da Adedipe yayi ikirarin cikewa baya cikin fayil din kotun

Daya daga cikin tawagar lauyoyin Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho a shari’arsa da ake yi na zambar kudade mai suna, Mista Adeola Adedipe, ya mika bukatar janyewa daga shari’ar.

Adedipe, wanda ke wakiltan kamfanin Maina, Common Input Property and Investment Limited ya sanar da kotu a yayinda zama kan shari’ar, cewa ya mika wata takarda.

Ya ce a cikin takardar da ya gabatar, ya bayyana kudirinsa na janyewa daga ci gaba da wakiltan wanda yake karewa wanda shine mutum na biyu da ake kara.

Lauya ya yi watsi da Abdulrasheed Maina, yana neman janyewa daga shari’arsa
Lauya ya yi watsi da Abdulrasheed Maina, yana neman janyewa daga shari’arsa Hoto: BBC.com
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Mutumin da matarsa ta haifi yan uku ya koka, ya roki yan Najeriya su kawo masa tallafi

Lauyan, ya bayyana cewa wanda yake karewa bai biya shi ba har yanzu, inda ya ba kotu hakuri a kan rashin kasancewarsa a wasu daga cikin zaman da aka yi a baya-bayan nan.

Alkalin da ke sauraron shari’ar, Justis Okon Abang , wanda a zaman karshe da aka yi ya bayyana cewa, bisa rashin bayyana a kotu, Adedipe ya yi watsi da zaman, ya bayyana cewa takardar da lauyan ke ikirarin ya gabatar baya a cikin fayil din kotun.

An dage sauraron shari’ar zuwa ranar 4 ga watan Disamba don ci gaba da zama, Channels TV ta ruwaito.

A gefe guda, babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, za ta saurari bukatar neman bayar da belin sanata mai wakiltan Borno ta Kudu, Ali Ndume.

KU KARANTA KUMA: Tsaida sunnah: Kebbi ce jihar da ta fi kowacce yawan maza masu auren mata 2 a Nigeria

An tsare Ndume a gidan yari tun ranar Litinin, kan tsayawa tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, da yayi, inda shi kuma ya tsere.

Maina na fuskantar tuhume-tuhume na zambar kudade har naira biliyan biyu kafin aka bayar da belinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel