Matashi yayi kokarin kashe kansa don an hana dan siyasan da yake so Tikiti a jihar Kano

Matashi yayi kokarin kashe kansa don an hana dan siyasan da yake so Tikiti a jihar Kano

- Don dan siyasa, wani mabiyi yai kokarin daukar rayuwansa

- Allah ya kiyaye an garzaya da shi asibiti cikin lokaci kuma ya sha da kyar

Wani matashi mai suna Abubakar Umar, dan karamar hukumar Rimin Gado a jihar Kano ya yi kokarin kashe kansa don an hana uban gidansa takara a zaben kananan hukumomin da ake shirin yi a jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa Umar ya sha maganin kwari da niyyar kashe kansa a daren Litinin.

Ya ce ya yanke shawaran kashe kansa ne domin an zabi wani dan takara daban wanda ba shi ya lashe zaben fidda gwani ba.

Ya ce shugaban karamar hukumar dake ci yanzu, Garba Shuaibu Rimin Gado, ya lashe zaben fidda gwanin inda ya samu kuri'u 35 cikin 43 amma duk da haka aka hanasa tikitin jam'iyyar.

"An yi zabe kuma ya samu kuri'u 35 cikin 43 kuma aka sanar ya yi nasara. Amma wasu munafukai suka ja hankalin gwamnan ya canza shi, " Umar yace.

"Babban bakin cikin shine wadannan mutane da aka baiwa ba su tare da gwamnan lokacin da yake fusktankar matsaloli a zaben 2019."

Matashi yayi kokarin kashe kan don a hana dan siyasan da yako so Tikiti a jihar Kano
Matashi yayi kokarin kashe kan don a hana dan siyasan da yako so Tikiti a jihar Kano Hoto: Tanko Yakassai
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sanata Ishaku Abbo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Bayani kan abinda ya faru, 'dan uwan Umar, Abdullahi Maikudi, ya ce an kira a waya da daddare cewa dan'uwansa yayi kokarin kashe kansa.

"Da na samu labari na garzaya wajen kuma muka tafi da shi asibiti a Rimin Gado. Bayan wasu allurai da suka bashi, sai aka tura mu asibitin Murtala Muhammed inda aka farfado da shi," yace.

Ya ce yanzu an sallamesu daga asibitin kuma yana murmurewa.

KU DUBA: Baka isa ka tafi da kujeranmu ba - Uwar jam'iyyar PDP ta gargadi Sanatan da ya sauya sheka APC

A wani labarin kuwa, jami'an hukumar yan sanda a jihar Anambara sun damke wata mata dake kokarin sayar da jaririnta na wata uku kudi N150,000.

Matar mai suna, Emila Sunday, ta shiga hannu ne a kauyen Ire, Ojoto, karamar hukumar Idemili south a jihar Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Tace matsanancin talauci da wahala ya sa ta haka, yan sanda suka bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel