An damke mahaifiya tana kokarin sayar da jaririnta kudi N150,000

An damke mahaifiya tana kokarin sayar da jaririnta kudi N150,000

Jami'an hukumar yan sanda a jihar Anambara sun damke wata mata dake kokarin sayar da jaririnta na wata uku kudi N150,000.

Matar mai suna, Emila Sunday, ta shiga hannu ne a kauyen Ire, Ojoto, karamar hukumar Idemili south a jihar Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Tace matsanancin talauci da wahala ya sa ta haka, yan sanda suka bayyana.

Tabbatar da haka, Kakakin hukumar yan sanda SP Haruna Mohammed, ya ce jaririn na cikin koshin lafiya, yayinda ake cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Cikakken bayani na kan tafe.....

An damke mahaifiya tana kokarin sayar da jaririnta kudi N150,000
An damke mahaifiya tana kokarin sayar da jaririnta kudi N150,000 Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel