Baka isa ka tafi da kujeranmu ba - Uwar jam'iyyar PDP ta gargadi Sanatan da ya sauya sheka APC

Baka isa ka tafi da kujeranmu ba - Uwar jam'iyyar PDP ta gargadi Sanatan da ya sauya sheka APC

- Uwar jam'iyyar ta nuna rashin amincewarta da sauya shekar daya daga cikin 'yayanta

- Wannan shine babban dan siyasa na biyu da zai bar PDP cikin kankanin lokaci

- PDP ta lashi takobin garzayawa kotu domin kwace kujerarta daga hannunsa

Uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta yi watsi da labarin sauya shekar Sanata Ishaku Elisha Abbo zuwa jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Uwar jam'iyyar PDP ta gargadeshi cewa ya sani za ta shigar da shi kotu kan hakan kuma bai isa ya tafi da kujerarta ba, rahoton Vanguard.

Mai magana da yawun PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya ce PDP bata damu da sauya shekan Sanata Abbo ba amma "ya san abinda kundin tsarin mulki ta tanada kan sauya sheka, kuma hakan shine ba zai iya cigaba da zama a kujerar a majalisar dattawa ba."

A cewarsa, "abinda kundin tsarin mulki ya tanada bayyane yake kan duk Sanatan da ya sauya jam'iyya kuma PDP ba zata bari Sanata Abbo ya tafi da kujerarta ba."

"Ba zai yiwu ba. Jam'iyyarmu ta fara kokarin maye gurbinsa da wani."

KU KARANTA: Za a fara sauraron bukatar bayar da belin Ndume a ranar Alhamis

Baka isa ka tafi kujeranmu ba - Uwar jam'iyyar PDP ta gargadi Sanatan da ya sauya sheka APC
Baka isa ka tafi kujeranmu ba - Uwar jam'iyyar PDP ta gargadi Sanatan da ya sauya sheka APC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Iyalan mai jaridan da dogarin Kakakin majalisa ya harbe sun bukaci N500m kudin diyya

Legit ta kawo muku cewa Sanata mai wakiltan Adamawa ta Arewa, Elisha Ishaku Abbo, ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, zuwa masu rinjaye All Progressives Congress, APC.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana sauya shekan Abbo a wasikar da ya karanta ranar Laraba a zauren majalisa.

A wasikar, Sanata Abbo ya yi bayanin cewa ya yanke shawaran sauya sheka daga PDP be saboda salon mulkin gwamnan jihar Adamawa, Umaru Ahmed Fintiri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng