An ci moriyar ganga: Ko kadan Buhari bai damu da arewa ba yanzu; ACF da NEF sun aika sako

An ci moriyar ganga: Ko kadan Buhari bai damu da arewa ba yanzu; ACF da NEF sun aika sako

- Ƙungiyar Dattijan Arewa (NEF) ta nuna damuwarta bisa matsalar tsaro da take addabar yankin arewacin ƙasar Najeriya.

- A cewar Ƙungiyar, ba ta gamsu da tafiyar kunkuru da aikin babban titin hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.

- Kazalika, Ƙungiyar tuntuba ta arewa (ACF) ta aika sakon fushin mutanen arewa zuwa ga Buhari, kamar yadda TheCable ta rawaito Emmanuel Yawe na fadi

Ƙungiyar Dattijan Arewa (NEF) ta ce gwamnati Shugaba Muhammad Buhari ta gaza yin kataɓus don kawo ƙarshen matsalar tsaron arewacin Najeriya.

A cewar jaridar The Guardian, ƙungiyar a wani jawabi da ta fitar ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba, ta zargi gwamnatin Buhari da yin burus tare da nuna halin ko in kula ga al-ummar yankin Arewa.

Kakakin ƙungiyar Dattijan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed, ya zargi gwamnatin Buhari da yin tafiyar kunkuru wajen aikin babban titin da ya haɗa jihohin Abuja, Kaduna da Kano.

KARANTA: 2023: Ba zamu taba lamunta a dauki Kirista daga arewa a matsayin dan takara ba; Jigo a APC, Farfesa Mahuta

Baba-Ahmed a kwana kwanan nan ya gano cewa aikin zai ɗauki tsawon shekaru biyar kafin a kammala shi.

Ko kadan Buhari bai damu da arewa ba yanzu; ACF ta aika sako
Ko kadan Buhari bai damu da arewa ba yanzu; ACF ta aika sako Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Kungiyar Dattijan Arewa tace akwai alamar tambaya,me yasa tun shekarar 2017 aka bada kwangilar titin amma ba'a fara aikin ba sai a shekarar 2018.

Tace tafiyar kunkurun da aikin babbar hanyar ke yi hujja ce ƙarara a fili dake nuni da cewa Shugaba Buhari bai damu da matsalolin da ke addabar yankin Arewa ba kwata kwata.

Ƙungiyar tace; "babban abin da ya damu shugaban ƙasa shine kuri'ar mu".

Wannan gwamnatin ta sake yankewa ƴan arewa hukuncin zama cikin halin ɗar-ɗar da barazana ga rayukansu tare da tattalin arziƙin yankin.

KARANTA: Sunayensu: Dangote ya shigar da karar wasu ma'aikatansa guda takwas

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, ƴan bindiga daɗi sun yi dirar mikiya a rukunin gidajen ma'aikatan jami'ar Zaria kuma sun ƙwamushe Farfesa, matarsa da ɗiyarsa.

Daraktan hulɗa da jama'a na jami'ar, Malam Auwalu Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin a jawabinsa a ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba.

Umar yace anyi musayar wuta tsakanin ƴan bindigar da jami'an tsaro.

Sai dai, ya ce 'yan bindigar sun saki mata da ɗiyar Farfesan a lokacin da jami'an tsaro suka kora su daji.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng