Sunayensu: Dangote ya shigar da karar wasu ma'aikatansa guda takwas

Sunayensu: Dangote ya shigar da karar wasu ma'aikatansa guda takwas

- Matsalar almundahana da badakala ba ga iya ma'aikatan gwamnati ta tsaya ba a Nigeria

- Kamfanin sarrafa Sukari na hamshakin attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya shigar da karar ma'aikatansa

- Ana zargin ma'aikatan takwas da wani dan kasuwa da laifin satar kudin da yawansu ya kai N451m

Rashin halartar wakilcin sashe na musamman mai yaƙi da zamba (SFU) na rundunar ƴansandan ya kawo tsaiko a ƙarar da kafanin sarrafa sukari na Dangote ya shigar da wasu ma'aikatansa.

A ranar Litinin ne aka fara sauraro karar a kan wasu ma'aikata guda takwas da wani ɗan kasuwa waɗanda ake zargi da satar zunzurutun kuɗaɗe Naira miliyan ₦451m daga kamfanin sarrafa sukari na Ɗangote.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ce ma'aikatan sun haɗar da; Musa Sule, Joseph Ukpah, Baba Tunde Ajao, Onyekwere Chinedu, Alayande Rahman, Omoro Ezekiel, Abugba Christian Odion da Mannir Mohammed.

KARANTA: NLC: Abin da ya fusata mu har muka fice daga tattaunawa da FG a kan karin farashin fetur

Sunayensu: Dangote ya shigar da karar wasu ma'aikatansa guda takwas
Sunayensu: Dangote ya shigar da karar wasu ma'aikatansa guda takwas
Asali: Facebook

Ana tuhumar dan kasuwa, Habib Mande, da kamfaninsa El-Habib Property Nigeria da sauran mutanen takwas da laifuka har guda takwas wanda suka ƙunshi; Tuggu, sata, yin jabun takardar Cek, da kuma amfani da takardun ƙarya.

A cewar tuhumar, waɗanda ake zargin, wanda suka aikata laifin daga shekarar 2012 da 2016 tare da Zainab Adebanjo,wanda suka haɗa kai suka ƙulla tuggun da yayi sanadiyyar sace Naira miliyan ₦451m mallakin kamfanin Dangote.

KARANTA: Buhari ya yi wa rukunin wasu ma'aikata gata, ya dauke musu biyan haraji

"A ranar 30 ga watan Nuwamba na 2015, da 7 ga Satumba, 2015 da 26 ga watan Afrilu na 2016, sun yi nasarar yin jabun takardar karɓar kuɗi mai lamba 132243, 132229, da 132279 bi da bi," a cewar wani bangare na tuhumar.

Lauyoyi masu kare waɗanda ake zargin, Messrs S. E Okeke, Ƙola Ƙadiri, da A.O Omodele sun nuna damuwarsu kan rashin halartar Emmanuel jackson zaman kotun.

Sun roƙi kotun kan ta yi duba da ƙwararan hujjojin waɗanda ake karewa tayi watsi da ƙarar sakamakon rashin takaimaimiyar hujja.

A kwanakin baya ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa kamfanin siminti na Dangote ya sanar da cewa ya samu izinin fitar da simiti ta kan iyakokin kan tudu zuwa kasar Nijar da Togo.

A watan Oktoban shekarar 2019, Shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya bada umarnin rufe kan iyakokin ƙasar domin kawo karshen safarar makamai, kayan abinci, da muggan ƙwayoyi zuwa cikin ƙasar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng