Bidiyo: ‘Yan sa-kai sun yi nasarar cafke masu satar mutane a titin Okene zuwa Lokoja

Bidiyo: ‘Yan sa-kai sun yi nasarar cafke masu satar mutane a titin Okene zuwa Lokoja

- Jama’a sun damke wadanda ake zargi suna garkuwa da mutane a Kogi

- ‘Yan sa-kai ne suka kama wadannan miyagu a kan titin Okene-Lokoja

- Dama masu garkuwa da mutane sun fitina mutanen dake wannan yankin

Labari mai dadi ya zo mana cewa wasu daga cikin ‘yan bindigan da su ka hana Bayin Allah sakat a arewacin Najeriya sun shiga hannu.

Gidan talabijin na TVC News ya fitar da wani bidiyo a yau ranar Litinin da ke tabbatar da cewa an yi ram da wasu miyagu a jihar Kogi.

An damke wadannan masu garkuwa da mutane ne a kan hanyar Okene zuwa garin Lokoja, Kogi.

KU KARANTA: N500, 000 ta raba ‘Daliban ABU Zaria da ‘Yan bindiga

Kamar yadda bidiyon ya nuna, an kama mutanen da ake zargin suna tare jama’a domin su karbi kudin fansa ne a kan wannan babban titi.

‘Yan banga da su ke aikin sa-kai ne su ka yi sa’ar kama wadannan miyagu da ake zargi da laifin garkuwa da mutane a yankin na jihar Kogi.

A bidiyon, za a ga mutane biyu a kwance yayin da guda ke zaune. Daga baya dukkaninsu sun mike inda za a gansu a galabaice suna cin abinci.

Wadannan mutane akalla uku sun yi zu-gum, yayin da a gefensu za a iya ganin wayoyin salula da dukiyoyin da su ka karbe daga hannun jama’a.

KU KARANTA: 'Yan bindiga na yawo da jerin sunayen mutanen da za su kashe

Bidiyo: ‘Yan sa-kai sun yi nasarar cafke masu satar mutane a titin Okene zuwa Lokoja
Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare Hoto: edition.cnn.com
Asali: UGC

Wanda ya dauki wannan bidiyo ya shaida cewa wannan abu ya faru ne a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba, 2020.

Babu alamun da ke nuna an far wa wadanda ake zargin. Za a dai a rika ganin motoci su na ta wuce wa, amma babu wani jami’in tsaro a wurin.

Dazu kun samu labari Dakarun soji sun kashe 'yan bindiga rututu a jihar Zamfara. Za a ga hotunan wadannan miyagu da suka yi mummunan karshe.

Rundunar sojin Najeriya ta yi gagarumar nasara a aikin da take yi na ganin bayan 'yan bindiga da miyagu a yankin arewa maso yammacin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng