Magu: Yau Kwamitin Ayo Salami zai mika rahoto game da binciken EFCC
- A yau kwamitin binciken Ayo Salami zai ba shugaban kasa rahoton aikinsa
- Ayo Salami da ‘yan kwamitinsa sun binciki zargin da ke kan Ibrahim Magu
- Ana sa ran tsohon mukaddashin shugaban na EFCC ya san matsayarsa yau
Idan abubuwa su ka tafi daidai, a yau Juma’a, 20 ga watan Nuwamba, 2020, za a gabatar da sakamakon binciken da aka gudanar a kan aikin EFCC.
Tun a watan Yuli shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti karkashin Ayo Salami domin ya binciki zargin da ke wuyan Mista Ibrahim Magu.
Rahotanni daga jaridar Vanguard sun bayyana cewa an ga ‘yan kwamitin Salami a fadar shugaban kasa dauke da tulin takardun binciken da su ka yi.
KU KARANTA: Laifuffuka 10 da ake zargin Magu da aikata wa a EFCC
Majiya daga Tribune ta shaida cewa tun a ranar Alhamis, Alkali Ayo Salami ya fada wa manema labarai sun karkare aikin da shugaban kasa ya sa su.
Tsohon Alkalin babban kotun daukaka karar ya fada wa ‘yan jarida cewa abin da su ke jira kawai shi ne shugaban kasa ya karbi rahoton aikinsu a yau.
Kawo yanzu ba a samu burbushin abin da rahoton binciken kwamitin shugaban kasar ya kunsa ba.
Idan za ku tuna, da farko mai girma shugaba Muhammadu Buhari ya ba kwamitin kwanaki 45 ne domin ya kammala bincikensa, ya gabatar da rahoto.
KU KARANTA: Malaman Jami’a sun bankado boyayyun dukiyoyin AGF a Kano
A karshe dole aka kara wa kwamitin wa’adi bayan ya bukaci karin lokaci a tsakiyar aikin na su.
An yi dace kwamitin zai gabatar da rahotonsa a daidai ranar da tsohon shugaban EFCC na farko, Nuhu Ribadu ya ke shirin bikin cika shekaru 60 a gobe.
Hukumar AMCON ta sa kafar wando daya da Attajiri, Jimoh Ibrahim a kan tulin bashin da ake bin shi. Bankuna suna bin Ibrahim kusan Naira biliyan 70.
Bashi ya yi wa attajirin yawa, a dalilin haka kamfanoni da asusunsa za su koma hannun gwamnati.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng