Kotu ta daure Isreal Ogundipe bayan samun shi da laifin sata a Legas

Kotu ta daure Isreal Ogundipe bayan samun shi da laifin sata a Legas

- Kotu ta samu Fasto Isreal Ogundipe da laifin satar kudin wata mata a kasar waje

- Ogundipe shi ne shugaban cocin Genesis Parish of the Celestial Church of Christ

- Limamin zai yi zaman shekara daya a gidan yari bayan an same shi da laifin sata

Alkali ya daure shahararren malamin addinin kiristan nan, kuma shugaban cocin Genesis Parish of the Celestial Church of Christ, Isreal Ogundipe.

Jaridar Punch ta ce an samu limamin kiristan da laifin satar dukiyar wata Baiwar Allah, a dalilin haka, kotu ta yanke masa daurin shekaru a kurkuku.

Babban kotun jihar Legas da ke zama a Ikeja ya samu Fasto Isreal Ogundipe da maida dukiyar wata mata a matsayin na shi da kuma laifin aikata sata.

KU KARANTA: 'Yan Sanda ba za su tsaya ayi ta kashe su ba - Kwamishina

A karshe Isreal Ogundipe wanda ake tuhuma a kotu tun shekarar 2011 da zargin aikata laifuffuka bakwai ya san makomarsa a hannun Olabisi Akinlade.

Alkali mai shari’a Olabisi Akinlade ya ce hujjoji sun gamsar da shi wannan malamin addini ya aikata biyu daga cikin laifuffukan da ake zarginsa da su.

A kan kowane laifi, faston zai yi zaman shekara guda a gidan maza. Hukuncin za su yi aiki ne a tare don haka Isreal Ogundipe zai fito bayan shekara daya.

Kotu ba ta samu faston da laifin bada bayanan karya, tursasa a bada kudi da bada shaidar bogi ba.

KU KARANTA: Tsohon Jigon PDP zai yi zama a gidan yari

Kotu ta daure Isreal Ogundipe bayan samun shi da laifin sata a Legas
Fasto Isreal Ogundipe Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A hukuncinsa, Alkali Akinlade ya umarci wanda ake kara ya biya Naira miliyan 11 ga wanda ta shigar da kara, Oladele Williams-Oni da ke zaune a Ingila.

Lauyan da ya tsaya wa wannan mata, Rotimi Odutola, ya ji dadin wannan hukunci da Alkali ya yi, ya ce Ogundipe ya karbi kudi daga hannun Williams-Oni.

Dazu da safe kun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yya karbi cikakken sakamakon binciken da aka dade ana gudanarwa kan Ibrahim Magu.

Ana sa ran tsohon mukaddashin shugaban hukumar na EFCC ya san matsayarsa a yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel