Dakarun soji sun kashe yan bindiga masu tarin yawa sun kwato makamai a Zamfara (hotuna)

Dakarun soji sun kashe yan bindiga masu tarin yawa sun kwato makamai a Zamfara (hotuna)

- Rundunar sojin Najeriya ta yi gagarumin nasara a aiki da take na kawar da miyagu a yankin arewa maso gabas

- Dakarun sojin sun yi artabu da yan bindiga a jihar Zamfara inda suka halaka da dama daga cikinsu

- Har ila yau sojin sun damke wasu mutane da ke hakar ma'adinai a jihar ba bisa ka'ida ba

Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa dakarun Operation Accord sun yi gagarumin nasara a mayar da hankali da suka yi wajen yaki da miyagu a yankin arewa maso gabas.

Dakarun sojin a ranar 21 ga watan Nuwamba, yayinda suke gudanar da aiki a kauyen Galadi da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara, sun yi kicibis da yan bindiga, a kan haka suka kashe yan bindiga biyu yayinda suka kwato bindigogin AK47.

Har ila yau, dakarun a yayin wani aikin kakkaba a kauyukan Sabon Tunga da Tamuske sun halaka yan bindiga da dama, sun ceto wasu mutum uku da aka yi garkuwa da su.

Dakarun soji sun kashe yan bindiga masu tarin yawa sun kwato makamai a Zamfara (hotuna)
Dakarun soji sun kashe yan bindiga masu tarin yawa sun kwato makamai a Zamfara Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Dakarun sojin da taimakon jirgin yakin sojin sama, sun tayar da wasu mafakar yan bindiga a Dutsen Emai da ke jihar Zamfara.

KU KARANTA KUMA: Za mu farauto makasan Shugaban APC na Nasarawa, Gwamna Sule ya sha alwashi

A wani lamarin kuma, duk a wannan rana, dakarun sojin yayinda suke fatrol a kauyen Gobirawa, sun yi arangama da yan bindiga. A yayin arangamar, an kashe yan bindiga shida yayinda aka kwato bindigogin AK47 guda hudu, bindigar toka uku da babura biyu.

A gefe guda, bayan samun bayanan sirri kan ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a Kadauri da ke karamar hukumar Maru, an tura dakarun soji yankin.

cikin haka ne dakarun sojin suka kama mutane 11 da ake zargi da hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.

KU KARANTA KUMA: Mayakan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya shida a Borno

An mika wadanda ake zargin ga hukumomin da ya kamata domin ci gaba da bincike, kamar yadda hedkwatar tsaro ta sanar a shafinta na Twitter.

A wani labarin, al’umman kauyen Aljumma a jihar Zamfara sun bayyana cewa yan bindiga sun tarwatsa su bayan wani hari da suka kai masu a ranar Lahadi.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa wani mazaunin kauyen ya sanar da ita cewa yan bindigar fiye da 50 sun kai farmaki kauyensu a kan babura sannan suka bude wuta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel