Bala Mohammed ya karyata rade radin sauya shekarsa zuwa APC

Bala Mohammed ya karyata rade radin sauya shekarsa zuwa APC

- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi watsi da jita-jitan cewa yana shirin jam'iyyar PDP zuwa APC

- Mohammed ya bayyana hakan a matsayin zance mara tushe balle makama

- Ya bayyana cewa a yanzu shi tunaninsa yana wajen ganin ya cika alkawaran zaben da ya daukarwa al'umman jihar Bauchi

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya karyata rade-radin cewa yana tattaunawa domin sauya sheka daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Ya karyata batun ne a cikin wata sanarwa da Mista Mukhtar Gidado, babban mai ba gwamnan shawara a kafofin watsa labarai ya saki ga manema labarai a Bauchi.

Ya saki jawabin ne a ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ku yi waje da mu idan kun gaji da ganin fuskokinmu, Lawan ga ‘yan Nigeria

An yi zargin cewa gwamnan na jihar Bauchi, yana daga cikin gwamnonin PDP uku da ke tattaunawa don komawa jam’iyyar APC, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Bala Mohammed ya karyata rade radin sauya shekarsa zuwa APC
Bala Mohammed ya karyata rade radin sauya shekarsa zuwa APC Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

“Muna fatan bayyana cewa labarin hasashe ne da wasu ke yi don cin kasuwarsu, domin ciyar da masu karatu wadanda sauya shekar gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi zuwa APC, ya rura wutar soyayyasu ga labaran siyasa.

“Muna kuma fatan sanar da cewa Gwamna Bala Mohammed bai taba tunanin barin PDP ba, balle ma har ya koma APC.

“Maimakon haka, a yanzu ya mayar da hankali wajen cika alkawaran zabensa, wanda a kansa ne mutanen jihar Bauchi masu karamci suka mara masa baya, domin ya kayar da gwamnatin da ke mulki a lokacin.

“Duk da rabuwar kai tsakanin bangaren zartarwa da na dokoki a jihar, wanda jam’iyyun siyasa daban-daban ke jagoranta, sun gina wani tsari na yin tarayya ta yadda gwamnatin jihar ta ke aiwatar da yaki da yunwa, gina ababen more rayuwa, gina fannin ilimi da ya kusa rushewa da kuma yaki da kananan laifuffuka,” in ji Gidado.

Gidado ya ci gaba da cewa gwamnan baya kowani tattaunawa game da sauya sheka zuwa wata jam’iyya sannan ya bayyana duk wani batu game da 2023 a matsayin kokarin janye hankali daga muhimman abubuwa.

“Don haka, Gwamna Mohammed na bukatar magoya bayansa da mambobin jam’iyyar siyasarsa da kuma mutanen jihar Bauchi masu karamci da su yi watsi da rahoton domin bai da tushe balle makama.

“Gwamnan na kuma fatan sake ba mutanen jihar Bauchi tabbacin cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali ne wajen tabbatar da rayuwa mai inganci ga dukkansu ba tare da la’akari da jam’iyya, jinsi ko kabila ba. "

A gefe guda, Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana cewa gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta fi alhairi fiye da shekaru 16 da gwamnatin Peoples Democratic Party (PDP).

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari gidan wani tsohon gwamna, sun kashe dan sanda

Umahi ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma'a a hirar da yayi a shirin Politics Today na tashar Channels TV.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel