An bada shawarar rage facaka da raba-kafa bayan tattalin kasa ya sake karyewa

An bada shawarar rage facaka da raba-kafa bayan tattalin kasa ya sake karyewa

- Masana sun yi magana a kan sake durkushewar tattalin arzikin Najeriya

- Kwararru irinsu Pat Utomi sun ba gwamnatin shawarar abin da ya dace

- An bada shawarar lafta haraji kan attajira domin a saukakewa Talakawa

Punch ta ce masana harkar tattalin arziki da kungiyoyin kwararru a Najeriya sun ba gwamnatin tarayya shawarar abin yi bayan an sake shiga cikin matsala.

Kwararru a sha’anin tattalin arziki irinsu Farfesa Pat Utomi da kuma Dr. Obadiah Mailafia a wata hira, sun bayyana yadda gwamnati za ta ceto tattalin Najeriya.

Daga cikin shawarwarin da masanan su ka ba gwamnatin Muhammadu Buhari shi ne ta cire haraji a kan talaka, sannan a raba kafa wajen samun kudin shiga.

KU KARANTA: Jihohin da su ka fi kowane arziki a Najeriya

Masanan sun ce dole gwamnati ta tashi-tsaye a game da maganar raba kafa wajen neman kudin shiga a yanzu da ake fama da rashin aikin yi da tulin bashi.

Kafin a je ko ina, Farfesa Pat Utomi ya na ganin dole sai gwamnati ta samu yardar al’umma. Daga nan kuma sai a rika kokarin kirkire-kirkire a Najeriya.

Pat Utomi ya ce Najeriya ta dogara ne da wasu, maimakon ta rika kirkirar na ta na kanta. Utomi ya kuma gargadi gwamnati game da tsadar kayan masarufi.

Shugaban ACCI, Adetokunbo Kayode da tsohon shugaban NERC, Sam Amadi suna ganin manufofin wannan gwamnati za su sake jefa kasar a matsala.

KU KARANTA: Sanatan Kaduna ya maida wa Ministan ayyka raddi

An bada shawarar rage facaka da raba-kafa bayan tattalin kasa ya sake karyewa
Buhari yana jawabi a Oktoba Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Sam Amadi ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya lafta haraji a kan attajirai, sannan a rage albashin manyan ma’aikata, sai a rage haraji a kan talakawa.

Dr. Bongo Adi ya nemi ga gwamnati ta rika jawo ‘yan kasuwa su na gina abubuwan more rayuwa. Sherrifdeen Tella ya bukaci a taimaki kananan ‘yan kasuwa.

A baya kun ji cewa Alhaji Atiku Abubakar ya na ganin cewa tun da tattalin arzikin kasa ya sake karye wa a wani karo, to kasafin kudin 2021 ba zai aiwatu ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, ya bada shawarwarin yadda za a farfado, daga ciki dole gwamnati ta hakura da facaka da kudin al'umma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel