Sanatan APC ya fusata da ministan ayyuka, ya alakanta kashe-kashe da miyagun tituna

Sanatan APC ya fusata da ministan ayyuka, ya alakanta kashe-kashe da miyagun tituna

- Sanata Uba Sani ya koka a kan munanan yanayin wasu titunan gwamnatin tarayya na jihar Kaduna

- A cewar Sanatan, matsalar titinan ne suke kara janyo kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar

- Don haka ne ya shawarci ministan ayyuka, Babatunde Fashola, da ya gyara titunan don taimakon rayuka

Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Mallam Uba Sani, ya alakanta hare-hare da garkuwa da mutanen da ake yi a jihar Kaduna da mummunan yanayin titunan gwamnatin tarayya na jihar, musamman titin Abuja zuwa Kaduna har Zaria.

Mai kawo wa Legit.ng rahotonni na Kaduna, Nasir Dambatta, ya tabbatar da yadda sanatan ya bayyana abinda yake zuciyarsa a kan gyare-gyaren da ya kamata a yi a jihar, a taron masu ruwa da tsaki da aka yi.

Ya nuna damuwarsa matuka a kan lalacewar titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria, ya nuna takaicin yadda gyaran titinan suke daukar lokaci mai tsawo.

A taron da ma'aikatar ayyuka ta shirya, wanda gwamnatin jihar Kaduna ta jagoranta, kuma Farfesa Ibrahim Gambari ya shugabanta a cikin jami'ar jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya roki Babatunde Fashola, da yayi gaggawar tabbatar da ayyukan titin gwamnatin tarayya na Kaduna. Saboda rashin kyan titinan ne suke sanya rayukan mutane a cikin hatsari.

KU KARANTA: Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace shugaban APC a Nasarawa

Sanatan APC ya fusata da ministan ayyuka, ya alakanta kashe-kashe da miyagun tituna
Sanatan APC ya fusata da ministan ayyuka, ya alakanta kashe-kashe da miyagun tituna. Hoto daga @ubasanius
Asali: Twitter

Kamar yadda sanatan ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, "Lalacewar titinan jihar ne suke saukaka wa miyagun mutane hanyoyin kai wa mutane farmaki. Ya kamata a ce an bayar da muhimmanci wurin gyaran titunan Abuja zuwa Kaduna, zuwa Zaria har Kano, cikin gaggawa don taimakon al'umma."

KU KARANTA: Tsame ASUU daga IPPIS na wucin-gadi ne, ba dindin bane, Ngige

A cewarsa, "Ya kuma kamata a ce an gyara titin Kaduna zuwa Birnin Gwari da kuma babban titin Nnamdi Azikwe. Mun gaji da kashe-kashen da ake yi a jihar Kaduna.

"Na samu labarin yadda kamfanin Dangote yake so yayi gyaran, har takarda sun tura wa ma'aikatar ayyuka amma shiru ba a basu dama ba, don haka yakamata a gaggauta ba su dama."

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya musanta labarin kai masa hari da 'yan ta'adda suka kara kai wa tawagarsa.

"Ba a kai masa hari ba, balle tawagarsa," kamar yadda Malam Isa Gusau, hadimin Zulum na harkar watsa labarai ya sanar a wata takarda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel