Garkuwa da mutane: Sai an bada N100m, za a fito da Jami’an ASP da ke tsare

Garkuwa da mutane: Sai an bada N100m, za a fito da Jami’an ASP da ke tsare

- ‘Yan bindiga suna neman N100m a kan Jami’an ‘Yan Sanda 6 da su ka sace

- Abin da Iyalan wadannan Jami’an tsaro za su tattaro ba zai iya wuce N3m ba

- An sace ‘Yan Sandan ne bayan an yi masa sauyin wurin aiki zuwa Maiduguri

Miyagun ‘yan bindigan da ke tsare da jami’an ASP shida na ‘yan sanda a jihar Katsina sun sa kudin fansar da za a biya kafin su samu ‘yanci.

Jaridar Punch ta ce ‘yan bindigan sun nemi a biya Naira miliyan 100 kafin su fito da wadannan jami’an tsaro da su ka yi fiye da mako guda a tsare.

Jami’an su na cikin wadanda aka tura aiki a garin Maiduguri, bayan an yi masu karin matsayi.

KU KARANTA: Yadda za a samu zaman lafiya a hanyar Kaduna-Abuja - Sani

A kan hanyarsu ta zuwa Zamfara ne aka tare su a yankin Dogon daji, tun daga wannan lokaci ba a sake jin duriyarsu ba sai a hannun masu satar jama’a.

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa jami’ai tara su ka shirya za su yi wannan tafiya zuwa Maiduguri, amma daga baya wasu cikinsu suka fasa.

“Lokacin da aka tare su, biyu sun kubuta, an harbi guda daga cikinsu a kafa, amma bai mutu ba. Ya samu kansa a wani kauye, har aka kai shi asibiti.”

“Ragowar shida suna hannun ‘yan bindigan har gobe, kuma ana neman miliyan 100 kafin a sakesu.”

KU KARANTA: 'Dan Majalisar Neja ya tsefe Buhari, ya ce Gwamnatin APC ta gaza

Garkuwa da mutane: Sai an bada N100m, za a fito da Jami’an ASP da ke tsare
Sufetan 'Yan Sanda Hoto: theeagleonline.com.ng
Asali: UGC

Iyalan wadannan Bayin Allah suna ganin ta kansu a halin yanzu, rahotanni sun ce suna neman hada Naira miliyan uku domin su fito da ‘yan sandan.

Ba a san ko idan iyalan kowanensu ya biya N500, 000 zai samu ‘yanci ba. Mafi yawan jami’an tsaron da aka kama, sune ke daukar dawainiyar gidajensu.

A makon nan kun ji irin wannan labari mai ban takaici inda ‘yan bindiga suka bukaci N270m kafin su saki wasu daliban ABU Zaria da aka sace a titin Abuja.

An tuntubi ‘yanuwan yaran da aka sace a hanyar Kaduna zuwa Abujan, an nemi su bada N30m.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng