Tsohon kwamishinan kudi na Abia Obinna Oriaku ya bar PDP
- Yan kwanaki bayan gwamnan Ebonyi ya bar PDP, wani babban jigon jam’iyyar ya sake sauya sheka
- Wani tsohon kwamishina a jihar Abia, Obinna Oriaku, ya yi murabus daga babbar jam’iyyar adawar kasar
- Sai dai, Oriaku bai yanke shawara a kan jam’iyyar siyasar da zai koma ba a nan gaba
Obinna Oriaku, tsohon kwamishinan kudi a jihar Abia, ya yi murabus daga babbar jam’iyyar adawa ta kasar wato Peoples Democratic Party (PDP).
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Oriaku ya sanar da shawarar da ya yanke ne a cikin wata wasika da ya gabatarwa da Shugaban PDP na gudunmarsa, Mbutu Ukwu Ward 3, Isiala Ngwa South, Owerrinta.
KU KARANTA KUMA: An kama wasu mutane biyu da suka yi wa dan sanda gashin tsire tare da cin namansa
Legit.ng ta lura cewa Oriaku ya kuma wallafa wasikar a shafinsa na Facebook.
Sai dai tsohon jigon na PDP, ya bayyana cewa bai riga ya yanke shawara a kan mataki na gaba da zai dauka ba a siyasance.
Tsohon kwamishinan ya yi bayanin cewa ya yanke shawarar barin PDP ne saboda jam’iyyar reshen jihar Abia bata da mutuncin da za ta isar da shugabanci mai nagarta.
Amma kuma, ya yaba ma gwamnan jihar, Okezie Ikpeazu, a kan karrama shi da yayi ta hanyar bashi damar yi wa al’ummansa hidima a gwamnatinsa.
KU KARANTA KUMA: Hotunan bikin auren dan gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, Bashir da amaryarsa Halima
A wani labarin, Shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, Philip Tatari Shekwo, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Emmanuel Bola Longe, wanda ya tabbatar da hakan a wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da jaridar Leadership, ya ce 'yan bindiga masu tarin yawa ne suka tsinkayi gidan shugaban APC.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng