Hotunan bikin auren dan gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, Bashir da amaryarsa Halima
- An daura auren dan gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai da amaryarsa Halima Nwakaego Kazaure
- Taron auren wanda ya gudana a Abuja a yau Asabar, 21 ga watan Nuwamba ya samu halartan manyan masu fada a ji
- Yan siyasa sun ajiye banbancin akida sannan suka dunga annashuwa da walwala a tsakaninsu
A yau Asabar, 21 ga watan Nuwamba ne aka daura auren dan gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai da amaryarsa Halima Nwakaego Kazaure.
Taron auren wanda aka yi babbar birnin tarayya Abuja ya samu halartan manyan masu fada a ji, sarakunan gargajiya da attajirai.
A hotunan bikin da aka wallafa a shafukan sadarwa, an gano mahaifin ango, Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai tare da matayensa cikin annashuwa da walwala.
KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun kai farmaki kusa da tashar jirgin kasa ta Kaduna, sun kashe mutum 1
Har ila yau an gano manyan mutane irin su tsohon sarkin Kano kuma aminin mahaifin ango, Muhammadu Sanusi II.
Daga cikin jami’an gwamnati da suka hallara akwai gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, tsohon gwamnan jihar Jigawa Mallam Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari, tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha.
Tsohon Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar Niger, Dr Babangida Aliu, Shugaban jam’iyyar PDP ta kasa, Uche Secondus duk sun hallara.
KU KARANTA KUMA: Bala Mohammed ya karyata rade radin sauya shekarsa zuwa APC
Ga karin hotunan auren a kasa:
Ga karin hotuna da shafin idon mikiya ya wallafa a Instagram:
Shafin maigaskiya ma a wallafa karin hotuna a shafinsa na Instagram:
A baya mun ji cewa, Bashir El-Rufai, daya daga cikin yaran gwamnan jihar Kaduna, ya haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya bayan ya wallafa hotunansa da amaryarsa a kan Twitter.
A cikin hotunan, an gano Bashir rike da kugun amaryarsa yayinda ita ma ta kamo shi cike da kauna.
A wani hoto kuma, an gano Bashir yana sumbatar amaryarsa a kumatu yayinda ita kuma ta rike fuskarsa tana murmusawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng