'Yan bindiga sun kai farmaki kusa da tashar jirgin kasa ta Kaduna, sun kashe mutum 1
- Mahara sun kai hari kusa da tashar jirgin kasa a jihar Kaduna a daren Juma'a, 20 ga watan Nuwamba
- Yan bindigan sun kashe wani bawan Allah sakamakon harbinsa da suka yi da bindiga
- Mazauna yankin sun bayyana cewa sun ga tashin hankali domin sun kasa bacci sakamakon musayar wuta da aka dauki lokaci ana yi
Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga sun kai farmaki yankin Rigasa da ke kusa da tashar jirgin kasa a jihar Kaduna a daren ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamba.
An kuma tattaro cewa maharan sun kashe mutum daya a harin.
Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa mazauna yankin sun ce basu iya sun yi bacci ba a daren jiya Juma’a din, cewa sun gudu cikin gari tare da iyalansu saboda harbe-harbe da aka kwashe tsawon lokaci ana yi tsakanin maharan da jami’an tsaro.
KU KARANTA KUMA: Bala Mohammed ya karyata rade radin sauya shekarsa zuwa APC
Rahoton ya nuna cewa wani mai suna Kwamared Muntari Sale ya ce an yi jana'izar wanda aka kashe sannan kuma cewa wani na nan kwance a asibiti sakamakon harbin da aka yi masa, sannan aka yi garkuwa da wani mutum daya.
"Sun zo da misalin karfe 8:00 na daren Juma'a a nan Titin Turaki kuma saboda muna kusa da wurin sai muka gudu cikin gari muka nemi mafaka," cewar Muntari Sale.
An tattaro cewa 'yan bindigar sun isa wurin ne a kan babura masu yawa, inda suka farfasa motocin 'yan sanda.
Zuwa yanzu gwamnatin Kaduna ba ta ce komai ba game da harin.
KU KARANTA KUMA: An kama matasa biyu dauke da akwatin gawa dankare da rigunan nono da dan kamfai na mata
A wani labari na daban, Yan bindiga sun harbe wani jami’in dan sanda har lahira a wani harin tsakar dare da suka kai gidan tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, da ke Toru-Orua a karamar hukumar Sagbama da ke jihar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa yan bindigan sun kai farmaki gidan Dickson ta kogin Forcados a daren ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng