An kama ƴan fashi da suka ƙware wurin kashe masu babur a Katsina

An kama ƴan fashi da suka ƙware wurin kashe masu babur a Katsina

- Ƴan sanda a Jihar Katsina sun cafke wasu matasa da ke kashe ƴan acaɓa bayan sun sace baburansu

- Asirin matasan ya tonu ne yayin da ake bincike kan fasa wani shago da aka yi sannan aka yi sata

- Yayin amsa tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa cewa sun kashe wani matashi sun sace babur ɗinsa an tafi da babur ɗin Nijar

Rundunar Ƴan sanda Jihar Katsina ta kama ƴan kungiyar fashi da suke ƙware wurin kashe masu acaɓa bayan sun ƙwace babur ɗin su.

Kakakin ƴan sandan jihar DSP Isah Gambo ne ya gabatar wa manema labarai wadanda ake zargin kamar yadda LIB ta ruwaito.

An kama ƴan fashi da suka ƙware wurin kashe masu babur a Katsina
An kama ƴan fashi da suka ƙware wurin kashe masu babur a Katsina. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An ceto rayuwar wata dattijuwa mai shekaru 80 da ta faɗa rijiya a Kano

Ya ce sunayensu sun haɗa da Surajo Lawal Na Kofar Guga Quarters, Hamisu Sama'ila da aka yi wa inkiya da Abu Kwalwa, da Habila Abubakar duk mazauna Sabon Gida Quarters a Katsina.

Ya ce dubunsu ya cika ne yayin da aka kama su a ranar 16 ga watan Nuwamba misalin ƙarfe 8 na dare yayin da ake binciken zargin fasa shago da sata.

KU KARANTA: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

"A yayin binciken wadanda ake zargin sun amsa cewa a ranar 14/11/2020 misalin ƙarfe 11 na dare, sun haɗa baki sun tare wani ɗan acaɓa, Yusuf Isiya mazaunin Farin Yaro Quarters a Ring Road Katsina suka kai masa hari da muggan makamai suka kashe shi suka tafi da babur ɗinsa ƙirar Hero da kudinsa ya kai Naira dubu ɗari da hamsin (N150,000:00K)", in ji Gambo.

"Har wa yau, wadanda ake zargin sun ce wani Anas Gagare, 25 da Danfakal, 26, (da ake kan nema) sun kai babur ɗin Maraɗi a Jamhuriyar Nijar. Ana cigaba da bincike," ya ƙara da cewa.

A wani labarin, Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya siffanta Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin 'raɓa' a yayin da ya ke tsokaci a kan wani littafi da aka rubuta kan shugaban kasar mai taken "The Buhari in Us".

Yahaya Bello ya furta hakan ne cikin wani faifan bidiyo da ya bazu a shafunkan sada zumunta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel