'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

- Bashir El-Rufai ya mayar da martani ga mutanen da ke sukar hotunansa da amarya Nwakaego

- A ranar Talata ne Bashir ya wallafa wasu hotunan tare da matar da zai aura inda a wani wurin ya rungume ta kuma ya ɗora hannunsa a ƙugunta

- Bashir El-Rufai ya ce masu sukarsa sakarkaru ne kuma ya gwammace a datse masa kai a maimakon ya nemi afuwar su

Bashir El-Rufai, ɗan gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce 'ya gwammace a datse masa kai a maimakon ya nemi afuwa' game da hotonsa da amaryarsa Halima Nwakaego Kazaure.

Tunda farko da an yi ta sukar Bashir saboda hotunansa da matar da zai aura da ya wallafa a Twitter.

'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙora', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa
'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙora', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Saudiyya ta bada guraben karatu 424 kyauta ga ɗaliban Najeriya, ta bayyana yadda za a iya samu

A hoton na farko da ya wallafa a ranar Talata - an gano shi ya ɗora hannunsa a ƙugun Halima yayin da a hoton na biyu kuma suna rungume da juna yana sumbatar kumatunta.

Sai dai wannan hotunan bai yi wa wasu mutane daɗi ba musamman wasu musulmi da ke ganin abinda da ya aikata haramun ne.

Da ya ke martani game da caccakar da wasu ke masa a ranar Laraba, Bashir ya ce masu sukar su faɗa masa idan akwai wani abu da zai iya yi don ya ƙara musu haushi.

KU KARANTA: Malamai a Kano na son a kafa dokar hukunta masu yi wa addini ɓatanci

'Idan hoto na da matata bai yi wa wasu dadi ba saboda shawararin da ban nema ba, ina son amfani da wannan damar in ce tabbas sakarkaru ne,' kamar yadda ya rubuta.

'Idan akwai wani hanya da zan iya ƙara ɓata musu rai, don Allah a sanar da ni. Wasu har yanzu ba su fahimci cewa ba kowa ne sukarsu ke tada wa hankali ba.'

Bayan wannan wani mai amfani da Twitter ya masa tambaya ya ce, 'Ina fatar ba za su saka neman afuwa ba don abinda ka faɗi.'

"Na gwammace a datse min kai a maimakon inyi hakan. Allah ya kyauta. Shashasha da ba za su iya fitowa su nuna kansu ba", Bashir ya bada amsa cikin gaggawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164