An ceto rayuwar wata dattijuwa mai shekaru 80 da ta faɗa rijiya a Kano

An ceto rayuwar wata dattijuwa mai shekaru 80 da ta faɗa rijiya a Kano

- Jami'an hukumar Kwana kwana sun yi nasarar ceto wata dattijuwa mai shekaru 80 da ta fada cikin rijiya a Kano

- Dattijuwar wacce ke zaune a Tundun Wuzurchi ta fada cikin rijiyar ne a yayin da ta ke kokarin diban ruwa

- Bayan sanar da su, jami'an hukumar sun garzaya inda abin ya faru inda suka ciro dattijuwar da ranta suka danka ta hannun dan uwanta

Hukumar kwana kwana na Jihar Kano, a ranar Juma'a, ta ceto wata dattijuwa mai shekaru 80 da ta fada a cikin rijiya a Tundun Wuzurchi a Municipal a Jihar Kano kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mai magana da yawun hukumar kwana kwana, Malam Saidu Mohammed cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, ya ce an kira hukumar daga Tundun Wuzurchi misalin karfe 6.40 daga wani Mallam Ibrahim Hussaini.

An ceto rayuwar dattijuwa mai shekaru 80 da ta fada rijiya a Kano
An ceto rayuwar dattijuwa mai shekaru 80 da ta fada rijiya a Kano. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

A cewar sanarwar, hukumar kwana kwanar ta aike da tawagar masu kashe gobara zuwa wurin, da isarsu wurin, sun gano cewa wata dattijuwa mai shekaru 80 ne ta fada cikin rijiya.

Sanarwar ta kara da cewa, "Jami'an na kwana kwana sun ceto dattijuwar da ranta, wacce ta fada cikin rijiya yayin da ta ke kokarin diban ruwa sannan suka mika ta hannun dan uwanta, Mallam Kabiru na Tudun Wuzurchi."

KU KARANTA: An aikewa masu nadin sarki 4 takardar tuhuma kan rashin halartar taron naɗin sabon sarkin Zazzau

A wani labarin, bala'i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel