Gwamna Yahaya Bello ya ce Buhari 'waliyyi' ne cikin wata faifan bidiyo

Gwamna Yahaya Bello ya ce Buhari 'waliyyi' ne cikin wata faifan bidiyo

- Gwamnan JIhar Kogi, Yahaya Bello ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari jinjina da yabo masu ban mamaki

- Yahaya Bello ya yi wa shugaban kasar wannan yabon ne yayin da ya ke sharhi kan wani littafi da aka rubuta game da Buhari mai taken 'The Buhari in Us'

- Gwamnan na Kogi ya siffan Buhari da ababe masu kyau da haske kamar 'raba' har ta kai ga ya ce Buhari ma 'walliyi' ne

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya siffanta Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin 'raɓa' a yayin da ya ke tsokaci a kan wani littafi da aka rubuta kan shugaban kasar mai taken "The Buhari in Us".

Yahaya Bello ya furta hakan ne cikin wani faifan bidiyo da ya bazu a shafunkan sada zumunta.

Gwamna Yahaya Bello ya ce Buhari 'waliyyi' ne cikin wata faifan bidiyo
Gwamna Yahaya Bello ya ce Buhari 'waliyyi' ne cikin wata faifan bidiyo. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

Gwamnan na Kogi ya kuma bayyana cewa Buhari mutum ne mai tausayi da halaye na gari, ta kai ga har ya bayyana shi a matsayin "waliyyi".

Ya kara da cewa Buhari yana da niyya mai kyau a zuciyarsa ga 'yan Najeriya kuma mutum ne mai karamci da tausayi.

KU KARANTA: Wike ya ce wani gwamnan PDP daya zai sake fita daga jam'iyyar

Har wa yau, Bello ya kara da cewa Buhari yana da masoya 'yan gani kashe ni' irin wadda ba za a iya samunsu da kudi ba sai dai matukar so da kauna ta gaskiya.

Ga dai faifan bidiyon a kasa:

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164