Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari gidan wani tsohon gwamna, sun kashe dan sanda

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari gidan wani tsohon gwamna, sun kashe dan sanda

- Wasu yan bindiga sun halaka wani jami'in dan sanda ta hanyar harbinsa a harin da suka kai gidan tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson

- Lamarin ya afku ne a daren jiya Laraba, 18 ga watan Nuwamba a gidansa da ke Toru-Orua a karamar hukumar Sagbama, Bayelsa

- Dan sandan ya kasance daya daga cikin tawagar tsaro na musamman da ke gadin gidan tsohon gwamnan

Yan bindiga sun harbe wani jami’in dan sanda har lahira a wani harin tsakar dare da suka kai gidan tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, da ke Toru-Orua a karamar hukumar Sagbama da ke jihar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa yan bindigan sun kai farmaki gidan Dickson ta kogin Forcados a daren ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya mika sakon gaisuwa ga tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayinda ya cika shekaru 63

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari gidan wani tsohon gwamna, sun kashe dan sanda
Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari gidan wani tsohon gwamna, sun kashe dan sanda Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Jami’in tsaron da aka kashe ya kasance daya daga cikin wata tawagar yan sanda na musamman da ke tsaron gidan tsohon gwamnan. An tattaro cewa ya mutu ne a nan take.

Da aka tuntubi kakakin yan sandan jihar, ya ce zai koro jawabi a kan lamarin a nan gaba.

A wani labarin kuma, wasu da ake zargin makasa ne sun kashe tsohon manajan kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Cif Gregory Duruiheakor.

An harbe Duruiheakor a gidansa da ke yankin New Owerri na Owerri, babbar birnin jihar Imo. Marigayin ya fito ne daga yankin Atta da ke karamar hukumar Njaba.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa yan daba sun kai farmaki gidan nasa a daren ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA KUMA: Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci sabon sarkin Zazzau, Nuhu Bamalli

Daya daga cikin yan uwansa ya tabbatar da lamarin. Ya ce: “Har yanzu muna cikin alhini game da mutuwar Cif Duruiheakor. Bayanai da muka samu ya nuna cewa an harbe shi ne a kirjinsa sannan ya mutu a nan take. Abun bakin ciki ne kuma mun kira yan sanda domin su gudanar da bincike a kan al’amarin."

Kakakin yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce Duruiheakor ya mutu kafin ya kai asibiti.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng