Gwamnatin APC ta fi ta PDP sau dubu, Gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka

Gwamnatin APC ta fi ta PDP sau dubu, Gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka

- Jihata ta fi samun romon demokradiyya karkashin Buhari fiye Obasanjo, Yar'adua da Jonathan, Umahi

- Ya yi jawabi kwana daya bayan sauya sheka daga tsohuwar jam'iyyar ta PDP zuwa APC

- Umahi ya kasance shugaban jam'iyyar PDP na jihar Ebonyi, sannan yayi mataimakin gwamna, kuma yanzu yana gwamna karo na biyu

Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana cewa gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta fi alhairi fiye da shekaru 16 da gwamnatin Peoples Democratic Party (PDP).

Umahi ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma'a a hirar da yayi a shirin Politics Today na tashar Channels TV.

"Idan ka kwatanta, ina ganin yan shekarun gwamnatin APC sun fi na tsohuwar jam'iyyata. Babu wani mai kama karya kan lamuran jam'iyyar," Umahi yace.

Umahi ya ce jihar Ebonyi ta amfana da APC cikin shekaru 5 da suka gabata fiye da yadda ta amfana da PDP cikin shekaru 16 da tayi mulki.

"Kowa na da zabi a rayuwa. Na zabi APC saboda suna gudanar da lamuransu da girmama shugaban kasa da kuma adalci ga dukkan gwamnoni," ya kara.

Wannan jawabi na gwamna ya biyo baya sauya shekar da yayi daga jam'iyyar PDP zuwa APC kuma jiga-jigan APC sukayi masa kyakkyawan tarba.

KU KARANTA: Gwamna Babagana Umara Zulum ya bude sabbin gidaje 50 da ya ginawa kananan malaman jami'ar UNIMAID

Gwamnatin APC ta fi ta PDP sau dubu - Gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka
Gwamnatin APC ta fi ta PDP sau dubu - Gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Wadanda suka halarci taron sauya shekarsa sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani; shugaban kwamitin rikon kwaryan APC kuma gwamnan Yobe, Mai Mala Buni; da gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar.

Sauran sune gwamnan Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu; gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello, dss.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta saduda, ta amince a cire ASUU daga IPPIS, ta bada N65bn kudin alawus

A ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamba, 2020, jam’iyyar PDP ta reshen jihar Ebonyi, ta dakatar da wasu daga cikin ‘ya ‘yanta, Vanguard ta rahoto hakan.

Jaridar ta ce jam’iyyar hamayyar ta dakatar da ‘ya ‘yan na ta ne saboda zargin su da ake yi da yi wa jam’iyya zagon-kasa da kuma wasu laifuffuka masu girma.

Wadanda aka dakatar sun hada da tsohon gwamnan jihar, da kuma duka ‘yan majalisar tarayya masu ci da su ka fito daga Ebonyi, da kuma wasu kusoshin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng