Yarinya 'yar shekara 9 ta nutse a rijiya bayan ta faɗa yayin ɗiban ruwa

Yarinya 'yar shekara 9 ta nutse a rijiya bayan ta faɗa yayin ɗiban ruwa

- Wata yarinya mai kimanin shekaru 9 ta rasu a kauyen Kwagar Kanawa da ke karamar hukumar Gezawa a Kano

- Yarinyar da ba sanar da sunanta ba ta fada rijiya ta nutse ne a lokacin da ta ke kokarin diban ruwa a gida

- Jami'an Kwana Kwana sun iso gidan sun ciro ta a sume amma daga bisani aka tabbatar da cewa ta riga mu gidan gaskiya

Wata yarinya mai shekara 9 ta riga mu gidan gaskiya bayan ta fada cikin rijiya ta nutse a yayin da ta ke kokarin diban ruwa a rijiya a gida.

Lamarin ya faru ne a unguwar Kwagar Kanawa a karamar hukumar Gezawa ta Jihar Kano kamar yadda LIB ta ruwaito.

Yarinya 'yar shekara 9 ta nutse a rijiya bayan ta fada yayin ɗiban ruwa
Yarinya 'yar shekara 9 ta nutse a rijiya bayan ta fada yayin ɗiban ruwa. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana ta JIhar Kano, Malam Saidu Muhammad wadda ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa a ranar Juma'a 20 ga watan Nuwamba ya ce ofishin 'yan sanda na Gezawa ya sanar da su abinda ya faru misalin karfe 8 na safe a Kwagar Kanawa.

Ya bayyana cewa sun aika jami'ansu ba tare da bata lokaci ba amma ko da suka iso sun tarar da cewa yarinyar da aka ce shekarun ta 9 da haihuwa ta rasu.

Yarinya 'yar shekara 9 ta nutse a rijiya bayan ta fada yayin ɗiban ruwa
Yarinya 'yar shekara 9 ta nutse a rijiya bayan ta fada yayin ɗiban ruwa. Hoto daga @lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: A dena kira na 'Special One', Mourinho ya bayyana sabon sunan da ya ke so

"Jami'an hukumar mu sun isa wurin da abin ya faru kuma sun gano cewa wata yarinya mai kimanin shekaru 9 ta fada cikin rijiya a yayin da ta ke diban ruwa. An ceto ta a sume sannan daga bisani aka tabbatar ta mutu.

"An mika gawar ta ga dagajin kauyen mai suna Alhaji Abubakar Usman na kauyen Kwagar Kanawa," in ji shi.

A wani labarin, an kama wata mata mai shekaru 40 da haihuwa mai suna Ruqayya Rabi'u a Jigawa bayan samun ta da jabun kuɗade (dubu ɗai-dai guda 100 da ɗari biyar-biyar guda 76) a ƙaramar hukumar Birnin Kudu.

Wacce ake zargin dai ƴar asalin ƙaramar hukumar Bichi ne a Kano ta shiga hannu ne bayan ta siya man shafawa na N300 a kasuwa kamar yadda LIB ya ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel