An kama matar aure mai juna biyu da jabun nairori a Jigawa

An kama matar aure mai juna biyu da jabun nairori a Jigawa

- Ƴan sanda sun damƙe wata mata a Jigawa tare da kuɗaɗen jabu masu yawa

- Asirin matar ya tonu ne a lokacin da ta tafi kasuwa siyan man shafawa a Birnin Kudu

- Matar ta ce wata daban ne ta bata kudin don ta siyo hatsi su raba ribar kuma ta san na bogi ne

An kama wata mata mai shekaru 40 da haihuwa mai suna Ruqayya Rabi'u a Jigawa bayan samun ta da jabun kuɗade (dubu ɗai-dai guda 100 da ɗari biyar-biyar guda 76) a ƙaramar hukumar Birnin Kudu.

Wacce ake zargin dai ƴar asalin ƙaramar hukumar Bichi ne a Kano ta shiga hannu ne bayan ta siya man shafawa na N300 a kasuwa kamar yadda LIB ya ruwaito.

An kama mace mai juna biyu da jabun nairori a Jigawa
An kama mace mai juna biyu da jabun nairori a Jigawa. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

Kakakin rundunar ƴan sandan Jigawa, SP Abdu Jinjiri ya tabbatar da kama ta ya ce ana cigaba da bincike don gano sauran wadanda ake zargin.

Jinjiri ya ce;

"Bayan an ƙwace kuɗaɗen bogin, ta amsa cewa wata Ladidi a ƙaramar hukumar Bichi ce ta bata kudin duk da cewa bata san gidanta ba. Kuma ta bukaci ta tafi Birnin Kudu ta siyo hatsi sai su raba ribar.

KU KARANTA: Katin gayyatar ɗaurin auren Bashir El-Rufai da Nwakaego ya fito

"Ta kuma ce ta san kudin jabu ne amma tana bukatar kudi don mijinta ya tafi ya bar ta da ɗawainiyar yara uku yanzu wata shida kenan ba a san inda ya tafi ba."

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel